Bikin cika shekaru 40 da ɓarkewar yaƙin Falklands

Daga CMG HAUSA

Tun a karni na 19, tsibiran Malvinas dake ƙasar Argentina suka fuskanci mamayar Turawan mulkin mallaka na ƙasar Birtaniya. A ranar 2 ga watan Afrilu na shekarar 1982, Argentina ta gwabza yaki da Birtaniya domin kwace iko da yankunanta na Falklands. Yakin da aka kwashe kwanaki 74 ana gwabzawa, kuma daga ƙarshe Birtaniya ta yi nasara.

Ranar 2 ga watan Afrilu na bana ta kasance ranar bikin cika shekaru 40 da ɓarkewar yakin Falklands. Ko da yake, yakin ya riga ya shude, sai dai ba abu ne da za a iya goge shi a tarihin al’ummar ƙasar Argentina ba, musamman gwarazan ƙasar Argentinan da suka fafata a yakin.

Mai fassarawa: Ahmad