Bikin Sallah: Bukola Saraki ya yi wa ‘yan Nijeriya nasiha

Daga WAKILINMU

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya a Majalisa ta tara, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar idin babbar sallah ta wannan shekara, inda ya yi kira ga musulmin Nijeriya da su ci gaba da jin tsoron Allah, don shi ne sinadarin bunƙasar ƙasa.

Saraki ya bayyana haka ne a saƙon barka da sallah da ya fitar yau a garin Ilorin ta Jihar Kwara, wanda ke ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Yusuph Olaniyonu.

Ya ce, kamar dai shekarar da ta gabata, idin babbar sallah ta wannan shekara ma za a gudanar da ita ne cikin annobar korona, wanda ya hana Musulmi da yawa zuwa aikin Hajji a Ƙasa mai tsarki.

“Shi Idin Babbar Sallah yana alamta sadaukarwa ne da tsoron Allah da Annabi Ibrahim (AS) da ɗansa, Annabi Isma’il (AS) suka nuna. Idan gabaɗayanmu za mu kasance masu tsoron Allah, al’ummarmu za ta inganta.

“Ƙasarmu za ta bunƙasa matuƙar shugabanni za su ji tsoron Allan wurin ɗaukar matakan da suka dace don inganta rayuwar talakawa.

“Da tsoron Allah ne kawai shugabanni za su riƙa ɗaukar matakan da za su haifar da haɗin kai, zaman lafiya, adalci, daidaito da bunƙasar ƙasa. Haka nan idan sauran ‘yan ƙasa suka kasance masu tsoron Allah, za su yi tsayin daka wurin ganin shugabanni sun yi abin da ya dace.” Inji shi

Bukola Saraki wanda shi ne Wazirin garin Ilorin ya ƙara da cewa, wajibi ne ‘yan Nijeriya su yi addu’ar Allah Ya samar da kariya da nasara ga sojojin da ke fagen daga wurin yaƙi da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

“Ina addu’ar Allah Ya kawo wa Nijeriya mafita , Ya kuma ba ƙasarmu nasara a kan duk wata barazana da ke fuskantar ƙasar. Barkanmu da Sallah” inji shi.