Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewar, wani taron gaggawa da ya taso a Abuja shi ne dalilin da ya sa Gwamnan jihar, Umar Andullahi Ganduje ya rasa zaman karɓar gaisuwar sallah daga Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar don ƙarin haske kan abin da ya hana Gandujen zaman karɓar gaisuwar basaraken a matsayin wani ɓangare bikin Sallah a Litinin ɗin da ta gabata.
Sanarwar ta ce, a wannan rana, Ganduje ya halarci wani taron gaggawa da ya taso ne a Abuja inda ya haɗu da sauran takwarorinsa don tattauna abin da ya shafi ƙasa.
Garba ya ce, Ganduje ya yi sallar Idi tare da Sarki Aminu a masallacin Idin Ƙofar Mata, inda daga bisani ya ziyarci shi a Gidan Shattima ya kuma halarci Hawan Daushen da aka yi a Fadar Sarkin Kano a ranar Lahadi da rana kafin daga bisani ya tafi Abuja don halartar taron gaggawa.
Ya ƙara da cewa, halartar Ganduje taron ya zama wajibi ne kasancewar dukkan waɗanda suka cancanci wakiltarsa a wajen taron duk ba su nan, sun tafi aikin Hajji.
Haka nan, ya ce tun kafin ma Ganduje ya yi tafiyar, sai da suka tattauna da Sarki a kan babu Gaisuwar Sallah bana wanda dukkansu sun yi ittifaki a kan hakan, amma cewa Sarkin zai zagaya gari kamar yadda aka saba wanda Fadar Gwamnatin Jihar na daga cikin hanyoyin da zai bi ya wuce.
Don haka Kwamishinan ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa da gangar Ganduje ya ƙi zaman karɓar gaisuwar Sarkin, kana ya yi kira ga al’ummar jihar da kada su saurari batun da babu kamshin gaskiya a cikinsa wanda masharranta suka kitsa.