Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari na yini 2

Daga BASHIR ISAH

Domin bai wa al’ummar musulmin Nijeriya musamman ma’aikata, damar gudanar da shagulgulan bikin Sallah Ƙarama cikin nishaɗi da annashuwa, Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun gama-gari na yini biyu, Litini 2 zuwa Talata 3 ga watan Mayu, 2022.

Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin sanarwa da ta fito ta hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Shuaib Belgore a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola a ranar Alhamis.

Ministan ya yaba wa ƙwazo da sadaukarwar da ma’aikatan gwamnati ke nunawa a bakin aiki wanda a cewarsa, hakan ta ƙara wa Nijeriya tagomashi a idon duniya.

Sanarwar ta ce, “Aiki abu ne mai muhimmanci a rayuwa. Rayayye ne kadai ke iya aiki amma ban da matacce.

“Don haka nake kira ga ma’aikata da su ƙara himma a wajen aiki domin bai wa gwamnatin Buhari damar cim ma ƙudurinta na yi wa ƙasa da al’umma hidima yadda ya kamata.”

Da ya juya kan batun bikin sallah, Aregbesola ya buƙaci al’ummar Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen nuna ƙauna da taimakekeniya a tsakanin juna, kyautata maƙwabtaka, zaman lafiya da sadaukarwa kamar dai yadda Annabi Muhammad (SAW) ya karantar.

A ƙarshe, Ministan ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, gwamnatin Buhari ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi Nijeriya.