Bikin Sallah: Yadda mutum 10 suka mutu a haɗarin mota a Kwara

Daga WAKILINMU

Hukumar Kula da Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen jihar Kwara, ta ba da bayanin wasu mutum 10 sun rasu sakamakon mummunan haɗarin da ya rutsa da su.

Shugaban FRSC na Kwara, Mr Jonathan Owoade, shi ne ya tabbatar da aukuwar haɗarin ga manema labarai a Ilorin babban birnin jihar.

Owoade ya ce haɗarin ya rutsa da wata mota ce ƙirar Toyota Hiace mai lamba LND 742 XK, a hanyar Oko Olowo/Oloru da ke yankin Iyemoja a Ilorin sakamakon gudun wuce misali da direban motar ya yi wanda hakan ya saɓa wa dokokin tuƙi.

Haɗarin wanda ya yi ajalin mutum 10 ya auku ne da misalin la’asar a ranar Babbar Sallar da ta gabata.

Bayanan FRSC sun nuna baki ɗaya mutum 18 ne a cikin motar, inda mutum 10 suka rasu sannan 8 suka jikkata.

Owoade ya ce bayan faruwar ibtila’in jami’ansu sun kwashi waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Ayo da ke Okolowo da kuma babbar asibitin Ilorin, haka gawarwakin a nan babbar asibitin aka adana su.

A ƙarshe, jami’in ya nuna buƙatar da ke akwai masu tuƙi su riƙa tafiya a sannu, saboda a cewarsa hanyar lafiya a bi ta da shekara. Kana a riƙa kula da dokokin amfani da hanya yadda ya kamata.