Bikin Sallah: Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya taya Musulmi murnar Sallah

*Ya buƙaci a dage da addu’a

Daga WAKILINMU

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara, Mai Girma Dauda Lawal, ya aike da saƙon taya murna ga ɗaukacin al’ummar Musulmi na Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya bisa ganin ƙarshen watan azumin shekarar 1444 da kuma bikin sallah.

A wata takardar sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar wadda Sulaiman Bala Idris ya sa wa hannu, Lawal ya buƙaci al’ummar Jihar Zamfara su zage damtse wurin yin addu’o’i don wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa, watan Ramadana zaɓaɓɓen wata ne daga Allah (SWT) a matsayin watan yin azumi da kuma tsarkake zukata.

Sanarwar ta ce: “Ina taya ɗaukacin al’ummar Jihar Zamfara murnar wannan muhimmiyar rana mai albarka ta Idi, wanda shi ne ya kawo mu ƙarshen wata mai alfarma na azumin Ramadana.

“Sallar Idi rana ce ta farin ciki da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa irin ni’imar da Ya yi mana na ganin kammaluwar wata mai alfarma.

“Rana ce da za a gode wa Allah (SWT) da Ya ba mu ikon yin ibadar azumi kamar yadda addini ya umurta a cikin Al-Ƙur’ani mai girma. Mun yi ibada tare da sake samun kusanci da Allah.

“Jiharmu tana cikin matsanancin hali na buƙatar addu’a da fata nagari. Dole ne mu ƙaunaci juna. Haka nan kuma dole ne mu ci gaba da rayuwa da darussan da muka koya daga watan Ramadan, musamman ma zaman lafiya.

“Kada mu manta da ci gaba da yin addu’a a kodayaushe don ganin dawowar zaman lafiya a jiharmu mai albarka,” in ji sanarwar.