Bikini Ista: APCON za ta Maka Bankin Sterling a kotu bisa ɓatanci ga Yesu Al-Masihu

AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai cibiyar kula da harkokin tallace-tallace ta ƙasa (APCON) za ta maka Bankin Sterling a kotu kan wani saƙon taya murnar bikin Ista da bankin ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, wanda cibiyar ta APCON ta ayyana a matsayin cin fuska ga Yesu Al-Masihu. 

APCON ta bayyana saƙon taya murnar da bankin ya wallafa wanda yake kwatanta ɗaukakar Yesu ɗin da tashin fitaccen biredin Legas ɗin nan mai suna, ‘Agege bread’ a matsayin abinda bai kamata ba. A cewar ƙungiyar wannan saƙon na talla da Sterling ya wallafa ya yi gaban kansa ne ba tare da ya tuntuɓar ta ba. 

Wannan saƙo yana ƙunshe ne a cikin wata takardar manema labarai da ƙungiyar ta saki ranar Litinin ɗin da ta gabata, wadda take dauke da sa hannun Magatakarda, kuma shugaban zartarwa na APCON ɗin, Dakta Olalekan Fadolapo.

Inda a cikin takardar ƙungiyar ta nuna rashin jin dadi ta game da wannan kwatance da ta ce mai tayar da hankali da bankin Sterling ɗin ya yi, kuma ta sha alwashin za ta gurfanar da shi, kuma ta tabbatar an yi masa hukuncin da ya kamace shi. Kamar yadda jaridar Ingilishi ta  Nairametrics ta rawaito.

Hakazalika, ƙungiyar ta bayyana saƙon taya murnar Ista na bankin a matsayin kalmomin yamutsa yazo da ta da fitina. Sannan kuma ya keta dokar APCON na tuntuɓarta kafin fitar da duk wani saƙo na tallace-tallace. Don haka a cewar su, dole a gurfanar da bankin gaban kuliya don girbar abinda ya shuka.

Amma sai dai a wani cigaban labari a baya-bayan nan kuma da Nairametrics ɗin ta sake rawaitowa, Bankin Sterling ya ba da haƙuri ga al’umma game da wancan rubutu da ya wallafa a shafinsa na yanar gizo yana kwatanta ɗaukakar Yesu Al-Masihu da tashin biredin Agege.

 Wannan rubutu ya jawo ce-ce-ku-ce a yanar gizo, inda mabiya shafin bankin suka yi Allah wadai da wannan rubutu kuma suka nemi bankin ya sauke rubutun daga turakarsa ta yanar gizo. Sannan kuma bankin ya ba da haƙuri da wannan rubutun da suka kira da cin fuska ga mabiya addinin Kiristanci. 

Amma a wani rahoton kuma, APCON ta ce ba ta gamsu don Sterling ya cire rubutun kawai ya ba da haƙuri ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *