Daga BASHIR ISAH
Hamshaƙin ɗan kasuwar nan Aliko Ɗangote da takwaransa Bill Gates da ya kasance Shugaban Bill and Melinda Gates Foundation, sun taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cire tallafin man da ya yi haɗi da sauran nasarorin da ya samu ya zuwa yanzu.
Ɗangote ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da manema labaran Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan ganawarsu da Shugaba Tinubu a ofishinsa a ranar Litinin.
A cewar Ɗangote, ana sa ran cire tallafin ya zama mabuɗi na hanyoyin samun ƙarin kuɗaɗe ga ƙasa don bai wa gwamnati zarafin zuba jari a sauran fannoni irin su ilimi da ababen more rayuwa da sauransu, don amfanin talakawan ƙasa.
Ya ƙara da cewa, ziyarar ta musamman ce kuma wata dama ce ta labarta wa Shugaban Ƙasar harkokin Gidauniyar Bill Gates da ta Aliko Ɗangote, yayin da suke fatan Gwamnatin ta ƙara himma wajen inganta fannin kiwon lafiyar ƙasar.
A nasa ɓangaren, Shugaba Tinubu ya sha alwashin bai wa fannin kiwon lafiya tsaron ƙasar muhimmanci.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da ayyukan ‘yan kasuwar sun cimma nasara a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya, musamman kuma a ɓangaren yaƙi da cutar shan-inna, zazzaɓin maleriya, baƙon doro da sauransu.