Bill Gates ya buƙaci Nijeriya ta inganta hannun jarin cigaban al’umma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hamshaƙin attajirin duniya kuma Shugaban Gidauniyar Bill da Melinda Gates, Bill Gates, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta inganta saka hannun jari wajen samar da mafita mai kyau ga mutane ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron samar da ƙirƙire-ƙirƙire na matasa na Pan-African a ranar Laraba a Legas, a wani ɓangare na ziyarar da ya kai Nijeriya.

Taron yana da taken: “Ci gaban Afirka: Sake Ƙarfafa Matasa a Kimiyyar Ƙirƙirar Ƙirƙirar.”

Gates ta ce, Nijeriya na cike da haziƙan mutane da dama, amma ya yi nuni da cewa zai yi wuya a iya cika wannan damar idan ba su samu damar yin amfani da basirar su ba.

“Ba zai ba ka mamaki ba cewa gwamnatocin jihohin Nijeriya da na tarayya suna kashe kusan dala 10 kan lafiyar mutum a kowace shekara, idan aka kwatanta da dala 31 a yankin kudu da hamadar Sahara baki ɗaya.

“Shugabannin suna buƙatar yin babban tsarin kuɗi, wanda zai mayar da hankali kan inganta tsarin kiwon lafiya a matakin farko.

“Tabbatar da cewa an samar da ma’aikata da kuma samar da asibitoci, tabbatar da cewa yara sun samuballuran rigakafin da suke buƙata, duk wannan yana da matuqar muhimmanci don inganta lafiya da kuma buɗe duk wata damar da Nijeriya ke da ita,” in ji shi.

Gates ya ce, zai yi magana da gwamnati game da ƙara ɗaukar alƙawurran da suka yi a fannin noma da tsarin hada-hadar kuɗi na zamani.

A cewarsa, matasan Nijeriya sun nuna sha’awar cigaba, amma akwai buƙatar su arfafa wa shugabanninsu kwarin gwiwa wajen aiwatar da waɗannan alƙawurran.

“A karo na ƙarshe da na ziyarci Nijeriya a shekarar 2018, na yi magana da shugabannin gwamnati game da yuwuwar ƙasarku na samun cigaba.

“A wannan karon kuma ina son yin magana ne kan ƙirƙire-ƙirƙire a Nijeriya.

“Tun lokacin da nake matashi, ina rubuta wasu abubuwa na kwamfuta a sakandare, kuma daga baya na fara a Microsoft, na ji daɗin ƙirƙirarta domub na samar da wani abu mafi kyau ga mutane.

“Duk da haka, ’yan Nijeriya har yanzu suna fuskantar qalubale da dama da na yi magana game da shekaru biyar da suka wuce, kuma dole ne ku fuskanci taɓarɓarewar tattalin arziki da barazanar tsaro.

Gates ya ce, matasa masu hazaƙa suna da ƙarfi wajen ganin duniya ta inganta.

Ya ƙara da cewa, yawan matasan Nijeriya na tare da ƙwarewa da yawa da kuma sha’awar magance manyan matsaloli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *