Bincike kafin aure a Ƙasar Hausa: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Masu karatu sannunku da bibiyar filinmu na zamantakewa wanda kuke karantawa kowanne mako a wannann jarida taku mai farin jini, Manhaja.

A wannan mako za mu yi bayani a kan bincike kafin aure a ƙasar Hausa. Menene bincike kafin aure? Bincike wani abu ne da magabatan yaro ko yarinya da suka shirya yin aure suke yi kafin a kai ga amincewa da auren nasu. Iyaye kan himmatu wajen bincike don tabbatar da wanda yake zuwa wajen yarinyarsu nagartacce ne ko akasin haka. Yayin da su ma iyayen yaro ba a bar su a baya ba. Su ma za su shiga bin diddigi da asalin wadda ɗansu zai aura. Na san masu karatu mazauna wannan yanki na qasar Hausa shaida ne a kan haka.

Amma inda gizo yake saƙar kuma wanda mai karatau zai shaida a kan haka shi ne; sai bayan an gama binciken kuma sai ya dawo ya zama akwai ya babu. Wato shi da babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Hakan kuma ba ya rasa nasaba da yadda idan an yi binciken ba a barinsa ya zama alƙali wajen tabbatar da auren ko barinsa. Sau da yawa sakamakon binciken ba ya tasiri a kan iyayen ma’auratan. Sai ka ga an rabu da jaki kuma an koma ana dukan taiki.

Bincike dai a aure wajibi ne kuma musulunci ma ya yarda a yi bincike a kan waɗanda za a aura. Haka al’adar Hausa ma tun tale-tale yana cikin tsarinta na aure. Kuma bincike yana da matuƙar amfani. Da binciken kafin auren nan za a iya kawar da matsaloli da dama na zamantakewar aure.

Abubuwan da ake bincikawa a game da wanda/wacce za a aura:

*Addini da tarbiyyar wanda/wacce za a aura: wannan yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar aure. Sai namiji ko mace mai tarbiyya da addini ne suke iya ba wa yaran da aka haifa tarbiyya. Aboki/abokiyar zama mai addini su ne suka san haƙƙoƙin abokin zama. Kuma suke kare su a cikin halin zamantakewa.

*Asali: Akan so a san asalin wanda za a aura. Tare da tarihin zuriyyarsu. Domin bincike ya nuna, yaran da aka haifa sukan ɗauko halayyar kaka da kakanninsu na kusa da na nesa. Samun wani abun ƙi daga zuriyyar wanda/wacce za a aura yana sa a guji haɗa zuriyya da su. Saboda kowa ba ya son haxa nasaba da bara-gurbin mutane.

*Sana’a: Binciken sana’ar mijin da za a aura shi ma wani babban jigo ne a cikin binciken aure. Akan bincika a ga sahihancin sana’ar da saurayi yake yi. Domin a tabbatar da zai iya riqe matar da za a aura da ɗaukar nauye-nauyenta. Idan aka bincika saurayi ba shi da cikakkiyar sana’a za a iya hana shi auren.

*Lafiya: Ana binciken lafiyar ma’aurara kafin su yi aure. Saboda kada matsalar lafiyar da suke da ita ta shafi zuriyyar da za su samu. Misali ana gwajin ƙwayoyin halitta na ‘genotype’ saboda gudun haihuwar yara masu cutar amosanin jini wato ‘sickler’. Haka idan mai rukunin jini 0- ya auri mai rukunin jini 0+ ana iya samun ɓari a jere saboda illar da jinin uwar zai dinga yi wa jaririn da yake cikinta. Idan ba a tsaya an yi bincike ba sai a ɗauka iskokai ne ko kuma wata matsalar. Haka ana duba ciwuka kamar kuturta, hauka, rashin haihuwa da sauran cututtukan da akan iya gada.

*Abokai/ƙawaye: Ana bincike a kan irin abokai ko ƙawayen mata ko mijin da ake son a aura wa yarinya. Domin an yi ittifaƙin ƙawaye da abokai su ne suke wakiltar halayen mutum.

*Riƙon iyali: Idan mutum mai mata yana neman wata zai aura, ana bincike a kan yadda yake kula da iyalinsa. Wato yadda yake riƙe da sauran matansa na gida. Irin riƙon da yake wa sauran shi ne shaidar cewa yana da riƙon aure ko a’a.

Wuraren da ake zuwa domin yin binciken aure:
Wasu wuraren da ake zuwa don a yi bincike sun haɗa da:

*Gidansa: Ana zuwa gidan mutum ko na iyayensa domin a gano waye shi. Kuma yaya alaqarsa take da iyayensa da iyalinsa da kuma maƙwabtansa.

*Maƙwabta: Kusan wannan ce babbar hanyar da ake yin bincike. Yawanci masu bincike sun fi aminta da shaidar maƙwabta a kan mutum. Magabatan yarinya kan nemi sanin bayanai game da halayyarsa wajen maƙwabtansa.

*Masallacin da yake sallah: A kan yi tambaya a masallacin da yake sallah.

*Wajen sana’a: A kan yi bincike a wajen da yake sana’a. Domin a san ya yake mu’amala da abokan sana’arsa. Kuma a tabbatar da yana riqo da sana’arsa. Wasu kuma don a tabbatar da sana’ar da ya ce yana yi ta gaske ce ko kuma faɗa kawai ya yi.

*Abokai: Akan binciki mutum ta hanyar tambayar abokanensa. Duk da dai wani lokacin ba a fiye dogara da wannan hanyar ba. Domin abokin damo guza ne inji Bahaushe. Amma kuma duk da haka ana la’akari da halayen abokanka a matsayin mizani na auna nagartarka. Shi ya sa budurwa mai tarin ƙawaye ba ta fiye farin jini wajen magabatan namiji ba.

Waɗannan su ne wasu daga cikin wuraren da ake zuwa don bincikar mijin da yarinya ta samu kuma ake shirin yin aure. Amma inda gizo ke saƙar shi ne, shin binciken da ake yi, yana da wani tasiri wajen bayarwa ko hana wannan saurayi auren yarinyar? Abinda ya sa na jefo wannan tambayar shi ne. Na gani kuma na san mai karatu ma ba zai kasa sanin wani aure da aka nufi yi kuma aka yi bincike aka gano wata matsala da namijin. Amma duk da haka aka wuce aka yi auren. Wannan ba ƙaramar matsala ba ce.

Mun sani a rayuwar nan ba wanda yake ba da uzuri sama da Bahaushe. Musamman ma a kan mutumin da yake ƙauna. Kuma ba don kuɗi ba ba komai ba. Wani fara’a da hirarsa ma yana sa uba ya amince ya ba shi ‘yarsa. Wannan ya sa wasu iyayen ko da sun jajirce sun yi bincike a kan saurayin a gano gaskiya amma sai ya zo ya kalamance iyayen da surutusu kuma su amince da shi. Sai bayan an yi aure kuma gaskiya ta bayyana.

Allah ya sani da a ce ana ba wa binciken tasirin da ya kamata ya samu, da da yawa daga matsalolin aure ba za a same su ba. Su kansu mazan, sai sun fi ƙoƙari su zama na gari ko don gudun kada mugun halinsu ya sa a hana musu auren wata. Haka kuma da al’umma sai sun fi jin ƙwarin gwiwar su faɗi gaskiya duk ɗacinta a kan wanda ake bincike a kansa. Kuma ko da ba a zo binciken ba, waɗanda suka san saurayin ko mijin yana da wani aibu za su fito su faɗa saboda su kiyaye iyayen yarinyar daga kitso da kwarkwata. Ko ɗaukar kara mai cike da kiyashi.

Matsala ta biyu kuma idan manemin yarinya yana da abun hannunsa. Ba a fiye tsayawa dogon bincike a kansa ba. Saboda shi Bahaushe baban abinda yake dubawa a gidan aure shi ne ɗaukar nauyin iyali ta fuskar ci da sha da sutura da muhalli da lafiya. Indai mutum zai iya ɗauke wa ‘yarsa waxannan to zai iya aura masa ita. Ko da ko meye halayensa. ‘Yar Bahaushe a gidan mijinta duk azabar da take sha da rashin jituwar dake tsakaninta da mijinta ba a yarda auren ya rabu in dai sun san ba matsalar waɗancan abubuwan da na lissafa a baya. Ko ta komo gida, sai iyayen sun mayar da ita. Shi ya sa in dai ka ji bincike ya yi tasiri an ce za a fasa aure don an gano wani abu to matsalar ba za ta wuce ta rashin muhalli ko an gano ba shi da cikakkiyar sana’ar da zai ɗauki nauyin matar. Ko kuma idan mai mata ne an gano ba ya iya ɗaukar nauyin iyalansa.

In dai namiji ya cika sharuɗɗan sama, ana zargin ma duk wanda ya kawo kushensa a matsayin ɗan adawa ko ɗan baƙinciki mai hana raya sunnar Annabi (SAW). Shi ya sa mutane da yawa idan aka zo musu da tambaya a kan maƙwabci ko abokin aikinsu da suransu ba sa zagewa su faɗi gaskiya ko yana da aibu. Haka waɗanɗa suka san halayensa suna tsoron faɗa su ruguza sunnar da ake son shiryawa ko kuma saboda kada a ce musu suna baqin ciki. Sai su zuba wa iyayen yarinya ido kawai ‘jiki magayi’. Ni na ga auren ma da aka zo ka gaya wa iyayen yarinyar mijin da ‘yar za ta aura yana da cutar ƙanjamau. Amma suka yi biris saboda yana da kuɗi. Har cewa suka yi ‘yan baƙin ciki ne waɗanda suka faɗa ɗin. Kuma daga ƙarshe aka yi auren gaskiya ta fito.

Ban ce ba a samun maƙiya ba. Waɗanda za su kawo maganar ƙarya don su ɓata auren da ake so ƙullawa ba. Sannan akwai kuma kura da fatar akuya. Waɗanda duk binciken ka ba za ka iya gano aibunsu ba. Waɗannan muna ba da shawara sai a koma ga Allah a riɗi istikhara shi ne maganin matsalar. Bissalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *