Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa domin amfanin ‘yan jihar aka rushe randabawul ɗin gidan gwamnati da ke jihar.
Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin, ya fitar aka kuma raba wa manema labarai a ranar Laraba ta ce, gwamnati ba ta ɗauki matakin rushe randabawul ɗin ba sai da ta tuntuɓi masana inda aka tabbatar mata lallai ginin shataletalen ba shi da inƙanci, kuma akwai yiwuwar ya ruguje tsakanin 2023 da 2024.
Sanarwar ta ce, “An cika wa aikin ƙasa maimakon kankaren siminti da aka sani.
“Sannan ginin ya yi tsayi sosai da za a bar shi a gaban gidan gwamnati wanda hakan na hana ganin babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin, takura ce ga jami’an tsaron da ke gadin gidan.
“Bugu da ƙari, ƙalubale ne ga abubuwan hawa a yankin saboda girmansa, wanda hakan ke hana wa direbobi ganin gabansu yadda ya kamata.
“Don haka gwamnati ta ga dacewar rushe ginin da zummar sake gina wani da ya dace ba da ɓata lokaci ba don ba da damar ganin mashigar fadar gwamnati yadda ya kamata da walwala ga masu abubuwan hawa.”