Bisa shirin saƙi da cin zarafin mata na “EU-UN Spotlight Initiative”, mun samu gagarumin cigaba – Uwargidan Gwamnan Legas

Daga WAKILINMU

Uwargidan Gwamnan Jihar Legas, Dr. Ibijoke Sanwo-Olu, ta bayyana cewa, sakamakon goyon bayan da suka samu daga shirin Tarayyar Turai (EU) da Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) na yaki da cin zarafin mata, Jihar Legas ta samu gagarumin ci gaba wajen samar da al’ummar da kowace ‘ya mace za ta iya rayuwa ba tare da tashin hankali ko nuna mata wariya ba.

“Ta hanyar haɗin gwiwar da muka yi, mun sami ci gaba sosai wajen samar da al’ummar da kowace mace za ta yi rayuwa ba tare da tashin hankali da wariya ba.” Ta bayyana a wurin rufe shirin na ‘EU-UN Spotlight Initiative’ da aka ɓullo da shi don kawo ƙarshen cin zarafin mata tare da mika cibiyar da aka samu don wannan aikin ga gwamnatin Jihar Legas a ranar 17 ga Nuwamba 2023.

Bikin da aka gudanar a otal din Airport da ke Ikeja ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da suka haɗa da kungiyoyin farar hula, ɗaliban Sakandare da dai sauransu.

A cewar Misis Sanwo-Olu, wacce babbar mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin cikin gida Misis Motolani Ladipo ta wakilta, Jihar Legas ta ci moriyar haɗin gwiwa da kawo sauyi dangane da kawo ƙarshen cin zarafin mata tun bayan kaddamar da shirin na yaƙi da cin zarafin mata na Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya a shekarar 2019.

“Jihar Legas tare da goyon bayan sashen mata na Majalisar Ɗinkin Duniya, da UNDP, da UNESCO, UNFPA da kuma UNICEF a ƙarƙashin shirin yaki da cin zarafin mata, ta aiwatar da abubuwa da dama da suka shafi ayyukan gwamnati da suka haɗa da kafa dokoki da tsara manufofi da ke mayar da hankali kan samun adalci ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin mata.” Ta bayyana.

Uwargidan gwamnan ta yi imani game da nasarar yin aiki tare, inda ta jaddada mahimmancin magance musabbabin cin zarafin mata. Ta kara da cewa, “Bisa himma mai karfi a ɓangaren rigakafi, kariya, da tabbatar da samun muhimman ayyuka, haɗin gwiwa da shirin ‘EU-UN Spotlight Initiative’ yana samar da hanyar da ba za a bar mace babba ko yarinya wajen ci gaba ba a Jihar Legas.”

Kwamishiniyar harkokin mata da yaƙi da fatara ta Jihar Legas, Ms Cecelia Bolaji Dada, ta bayyana nasarorin da aka samu da kuma muhimman abubuwan da aka cimma a shirin na yaki da cn zarafin mata a Jihar Legas. Ta bayyana yadda suke ƙarfafa ayyuka masu mahimmanci ciki har da kafa asibitocin duba marasa lafiya ta shafin intanet a lokacin annobar COVID19; da ƙarfafa damar samun adalci ga waɗanda suka tsira daga cin zarafi, ƙarfafa yekuwar kungiyoyin mata, samar da tallafin gina rayuwa ga waɗanda suka tsira daga cin zarafi fiye da 300; da kuma samar da ɗakin da ake duba waɗanda aka ci zarafinsu wanda ya taimaka wajen samar da bayanai a kan shari’ar cin zarafin mata tare da wallafawa a cikin rahoton Ofishin Ƙididdiga na Ƙasa.

Babban alkalin jihar Legas, Hon. Kazeem Alogba, ya jaddada muhimmiyar rawar da ɓangaren shari’a ke takawa wajen magance cin zarafi da nuna wariya ga mata a Jihar Legas.

Da yake magana ta bakin Mai shari’a Abiola Soladoye, ya bayyana mahimmancin kin yin shiru kan abubuwan da suka shafi cin zarafi tare da karfafa wa waɗanda suka tsira daga aika-aikar su rika neman adalci ba tare da tsoro ba.

“Bai kamata a yi watsi da miyagun laifukan da ake wa mata ba, kuma idan aka ba da rahoton, waɗanda abin ya shafa ka da su yi shakka su fito su fada.” Yana mai bayyana cewa, “‘Yansanda suna da ruwa da tsaki tare da ɓangaren shari’a wajen taimaka wa daƙile lamuran da suka shafi cin zarafin mata.”

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya jaddada ƙudurin majalisar na yaƙar duk wani nau’in cin zarafin mata a jihar.

Wanda Hon. Princess Omolara Oyekan ta wakilta, shugaban majalisar ya jaddada cewa, “Majalisar ba ta ɗaukar duk wani nau’i na cin zarafin mata ta kowace hanya da sanya, sannan kafa hukumar yaƙi da cin zarafin mata ta Jihar Legas wani muhimmin mataki ne na sadaukarwar da majalisar ta yi don kawar da cin zarafin”.

Ya kara da cewa ƙoƙarin da majalisar dokokin Jihar Legas ta yi na samar da dokoki na kare haƙƙin mata ya sa manyan hukumomi irin su hukumar yaƙi da cin zarafin mata ta jihar Legas da ma’aikatar mata ta jihar Legas suka yi tsayin daka tare da tsre wa tsara kan kare hakkokin mata.