Biyo bayan zaɓukan fidda gwani…Shin Adamu zai iya saisaita al’amuran APC?

…Ko ya zo a makare ne?
…Ya zai warware sarƙaƙiyar takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa?
…Ta ina zai ɓullo wa rikicin takarar Ahmad Lawan da Machina?
…Shin Buni ya gadar ma sa kangarwar jam’iyya ne?
…Me ya sa Fadar Shugaban Ƙasa ke sakar ma sa ragama?

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Biyo bayan kammala zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, rikici da ficewa daga cikin jam’iyyar ya varko sakamakon yadda wasu da ke neman takara suke ganin ba a yi musu adalci ba ko kuma ba su samu abinda suke so ba.

Duk da cewa, wannan ba wani baƙon abu ba ne a cikin jam’iyyar da ake ganin za ta iya kai bantenta, musamman ma don kasancewarta mai riƙe da madafun iko. To, amma lamarin yana buƙatar direban asali kuma direban gaske, wanda zai iya jan sitiyarin motar jam’iyyar ga tudun mun tsira, duk da irin ƙalubalen da ta ke fuskanta.

Wasu na gani cewa, da tun tuni aka gudanar da zaɓen shugabancin jam’iyyar, Sanata Adamu ya zama shugabanta, wataƙila da yanzu ba a tsinci kai a haln da ake ciki ba. Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa, kamar Adamun ya zo a makare, saboda yadda tsohon Shugaban Riƙon Ƙwarya na Jam’iyyar kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ƙi sakin sitiyarin jam’iyyar da wuri har sai da al’amura suka rincave, sannan ya shirya zaɓukan jam’iyyar.

Wannan ya sanya Sanata Abdullahi Adamu ya zama tamkar ɗan kwana-kwana bayan da amshi ragamar mulkin jam’iyyar, saboda ya ɗare karagar ne ana dab da fara zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar. Don haka shi kansa bai ga daidaita sahunsa akan kujerar ba ya fara da ƙoƙarin sasanta rikicin cikin gida a matakai daban-daban.

Za a iya cewa, ɗan abinda ya taimaka masa ma shine, kasancewar ya shugabanci kwamitin sasantawa na jam’iyyar a baya, wanda ya ba shi damar sanin wasu matsalolin rigingimun tun daga tushe. Don haka ba yankan rake ba ne shi a cikin lamarin.

Haka nan, a fili ta ke cewa, Fadar Shugaban Ƙasa ba ta iya taka rawar da ya kamata wajen yayyafa wa rikicin da jam’iyyar APC ke fuskanta a halin yanzu, musamman don ganin yadda har aka kai ga gudanar da takarar fitar da gwani na APC a kowane mataki ba tare da ta iya saita mutanenta, don su lashe zaɓukan ba ta yadda idan rigingimu sun biyo baya, za a iya tsawatarwa, su ji.

Babban misali anan shine, yadda rikici ya ɓarke a Jihar Yobe kan takarar kujerar Santan Yobe ta Yamma, kujerar da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya sukutum, Sanata Ahmad Lawan, ya ke kai, amma yanzu ya ke fafutukar ganin ya sake samun tikitin jam’iyyar bayan da ake kyautata zaton Fadar Shugaban Ƙasa ce ta so ya yi takarar Shugaban Ƙasa, amma bai samu laseh zaɓen fitar da gwani ba.

Ana ganin cewa, aa a ce, Fadar Shugaban Ƙasa ta taimaka wa jam’iyyar yadda ya kamata wajen tsaya wa tsayin daka, Lawan zai iya samun tikitin takarar Shugaban Ƙasar, kamar yadda Marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya samu a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PDP lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ke mulki, ballantana kuma a dawo ana jan’injar takarar kujerar sanata da Lawan.

Haka zalika, ko da bai samu tikitin takarar Shugaban Ƙasa ba, abu ne mai sauƙi ya samu ta sanatan da ya ke kai, idan da a ce, tun asali an tyi kyakkyawan tsari, kamar yadda ya faru a jihohin Bauchi da Sokoto ga gwamnoninsu masu ci bayan da suka tsaya takarar Shugaban ƙasa a tutar PDP ba su samu ba.

Za a iya cewa, irin hakan ce ta sanya aka shiga halin ha’ula’i kan batun wanda zai mara wa ɗan takarar jam’iyyar na Shugaban Ƙasa a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa. Wasu na ganin cewa, idan da Adamu ya hau kan karagar shugabancin APC da wuri, ba za a zo wannan lokaci ba tare da an ɗauki alqibla tsayayyiya kan ɗan takarar Shugaban Ƙasa ba, ballantana na mataimaki.

To, sai dai kuma duk da waɗannan matsaloli, za a iya cewa, shekarun Sanata Abdullahi Adamu a duniya da kuma daɗewarsa a harkokin siyasa tare da gogewarsa za su iya ba shi dama ya iya warware waɗannan matsaloli, amma sai idan gwamnonin jam’iyyar ta APC sun ba shi haɗin kan da ya kamata.

Wasu na ganin cewa, gazawar Fadar Shugaban Ƙasa wajen ɗaukar alƙibla guda ɗaya ya bai wa gwamnonin ƙarfin da ya wuce gona da iri ta yadda hatta makusantan Shugaban Ƙasa ba su iya tsaya wa takara a jihohinsu su samu tikitin jam’iyyar, kuma hakan ba ya sanya wani abu ya biyo baya. Ma’ana,; Fadar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba ta nuna damuwarta kan yadda na hannun damanta suka riƙa faɗuwa a zaɓukan fitar sa gwani ba. Wannan ya ƙara bai wa gwamnoni ƙarfi kuma ya sanya APC ta rasa jagorancin da ya kamata a ce jam’iyya mai mulki na da ita.

Tabbas kasancewar Sanata Adamu tsohon gwamna kuma tsohon sanata, sannan attajiri ne, ya sanya zai yi wuya a iya yi masa taka-haye daga gwamnoni, to amma duk da haka yana buƙatar cikakken goyon baya daga Fadar Shugaban Ƙasa, idan har ana so ya iya ɗora jam’iyyar kan tafarkin da ya kamata.

Masana dimukraɗiyya da dama na da ra’ayin cewa, a siyasa, ɗaukar alƙibla ba laifi ba ne, kuma rashin ɗaukar alƙibla guda ɗaya rauni ne, wanda ya ke iya raunana jam’iyya komai ƙarfinta.

A zahirance, APC tana da jagoran da zai tuƙa sitiyarinta zuwa tudun min tsira, amma sai dai tabbas ya na da buƙatar fulogan da za su iya masa aikin da zai samu wutar da za ta iza hasken da ake buƙata!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *