Blinken ya tattauna da Tinubu ta wayar tarho don ƙara inganta hulɗar difilomasiyya tsakanin Nijeriya da Amurka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony J. Blinken, ya tattauna da Zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya Bola Tinubu.

Blinken ya kira Tinubu ne ta wayar tarho a safiyar Laraban nan da ta gabata, inda ya nuna zimmarsa na ganin Amurka ta qara ƙarfafa hulɗar dangataka da Nijeriya, musamman ma da gwamnati mai zuwa.

Ya ce ƙasashen biyu sun ɗauki tsawon lokaci suna hulɗa mai kyau, inda ya ce yana so ya ga ɗorewar hakan ƙarƙashin mulkin Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Tinubu.

Tinubu da Blinken sun kuma tattauna kan muhimmancin gudanar da gwamnatin da za tafi da duka ‘yan Nijeriya da ƙara inganta tsaro da kuma kawo tsare-tsare da za su taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.