Bokayen da suka damfari wani ɗan siyasa Naira miliyan 24 sun faɗa komar EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani ɗan siyasa ya yi ƙarar bokansa da malamin tsubbunsa a wajen Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC) kan zargin damfararsa bayan ya faɗi zaɓen neman takara.

Jami’an EFCC da ke Legas sun damƙe bokan da ɗan tsubbu, Alfa Abiodun Ibrahim da Wale Adifala ne, bisa zargin damfarar ɗan siyasar da yake neman kujerar Majalisar Wakilai a Jihar Ekiti da ba a bayyana sunansa ba Naira miliyan 24.

Jaridar PM ta ruwaito cewa waɗanda ake zargin sun bugi hancin ɗan siyasar ne cewa za su yi masa aiki ya ci zaɓen takarar ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, amma ya sha kaye.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya ce a ranar 7 ga Yulin 2022 aka damƙe su a Ado-Ekiti, Jihar Ekiti, bayan an kai ƙararsu gaban hukumar a kan abin da suka aikata.

Jami’in ya ce a lokacin da ake binciken su, bokan ya yi iqirarin ya karɓi kuɗaɗe daga hannun ɗan siyasar har ma da ƙarin Naira 2.9 a matsayin kuɗin sayen shanu da raguna da sauran kayan aiki.

Da yake mai da bayani, ɗan tsubbun ya ce, “namu bai wuce yin addu’o’i da yanka abin yanka ba, sannan mu bar wa Allah sauran.”
Uwujaren ya ce za a gurfanar da su biyun a kotu nan ba da daɗewa ba.

Adifala, ya amince ya amshi Naira Miliyan 2.9 don ya siyo baƙi, fari da jar saniya, raguna da kuma sauran kayan aikin da za su yi amfani da su. 

“Daga nan kuma na haɗa shi da wani malamin tsibbu, Ifawole Ajibola, wanda ya ci gaba da aikin da muke masa, har zuwa lokacin da muka shiga hannun EFCC,” inji shi.