Boko Haram sun karɓe Kaure har sun kafa tutarsu – Gwamna Bello

Daga AISHA ASAS

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya tabbatar da ‘yan Boko Haram sun shigo jihar Neja musamman ma a yankin Kaure da ƙaramar hukumar Shiroro, kuma har ma sun kafa tutarsu.

Gwamna Bello ya sanar da hakan ne sa’ilin da ya ziyarci ‘yan gudun hijira su sama da 3000 daga yankin ƙaramar hukumar Shiroro da Munya da suka yi sansani a harabar makarantar Firamare ta Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Minna.

A cewarsa, “Ina mai tabbatar da cewa akwai ɓurɓushin Boko Haram a Neja, a yankin Kaure.

“Na samu bayanin har sun kafa tutarsu a Kaure, wanda haka ke nufin sun karɓe ikon yankin, kuma wannan ne ya sa na yi ta bibiyar Gwamnatin Tarayya gudun kada abin ya ta’azzara amma tun da ya kai wannan matsayi, idan ba a yi hattara ba hatta Abuja ba ta tsira ba”.

Yan gudun hijira

Gwamnan ya koka kan irin matslar tsaron da jihar ke fama da ita, tare da nuna damuwarsa kan yadda ‘yan Boko Haram suka karɓe matan yankunan da lamarin ya shafa.

Ya ce, “‘Yan Boko Haram suna ƙoƙarin yin amfani da waɗannan yankuna a matsayin cibiyoyinsu kwatankwacin yadda suka yi a Sambisa.”

A cewar sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun sakatariyar yaɗa labarai ta gwamnan, Mary Noel-Berje, gwamnan ya ce wannan matsala aba ce da ke buƙatar haɗin kan kowa. Kana ya ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba game da matakan da ta ɗauka wajen daƙile matsalar.

Bello ya ce duk da dai bai cire tsammani daga Gwamnatin Tarayya ba, amma abin da ya sani shi ne ba zai ci gaba da zaman jiran kowa ba.

‘Yan gudun hijira

Wani mazaunin ƙauyen Kuchi a ƙaramar hukumar Munya mai suna Bulus Asu, ya ce baki ɗaya yankin Kuchi ya faɗa mummunan hali tun watanni uku da suka gabata.

Ya ce ‘yan bindigar kan shiga Neja ne daga Kaduna kuma ta ƙauyen Kapana inda sukan sace mutane tare da yi wa mata fyaɗe. Ya ci gaba da cewa ƙauyukan Kuchi, Guni, Gini, Chiri, Fuka da kuma Kapana na daga cikin wuraren da suka sha fama da ‘yan fashin dajin tun shekaru uku da suka gabata.