Boko Haram sun yi awon gaba da wasu fasinjoji 35

Akalla ana zaton kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun yi awon gaba da wasu fasinjoji har 35, a yayin da wasu su ka samu raunuka, wasu kuma su ka tsere cikin daji.

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewa, wannan abu ya auku ne a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, bayan da yan Boko Haram din su ka tare hanya, suka kona wasu motoci ciki har da wata babbar mota mallakar kamfanin Dangote.

Jami’an yan sanda dai sun shaidawa manema labarai cewa, a halin da ake ciki, an kwato mutum goma, sannan wadanda su ka ji raunuka kuma an kai su asibiti.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*