Boko Haram ta kashe jami’ai biyu a harin da ta kai wa ofishin ƴan sanda a Borno

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an ƴan sanda biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin boma-bomai da wasu mayaƙan Boko Haram suka kai a ofishin rundunar da ke garin Gajiram na ƙaramar hukumar Nganzai a Jihar Borno.

Haka ma wani jami’in ƴan sandan ya samu mummunan rauni a yayin da aka yi ba-takashi tsakanin ɓangarorin biyu inda a lokacin ne jami’an haɗaka na CJTF da ke kusa da ofishin suka kawo ɗauki tare da fatattakar ƴan ta’addar.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta ce mayaƙan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Laraba.

Ta ce babu wani waje ko kayan aiki na jami’an da aka salwantar a yayin farmakin.

Saidai, wata sanarwar da ƴan sanda ta fitar ta Kakakinta na jihar, Kenneth Daso, ta ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:10 na asubahin ranar Alhamis.

Ya kuma ce an gano wasu gurnet-gurnet na hannu guda biyu a wajen da al’amarin ya faru a lokacin da Kwamishinan ƴan sandan jihar, Yusufu Lawal ya kai ziyarar gani da ido a yankin.

Kwamishinan ya jinjina wa jami’an da suka tsaya wajen mayar da martani ga harin tare da jajenta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a lokacin harin.

Ya ƙara da cewa, rundunar za ta cigaba da ƙoƙarin bai wa al’umma kariya da samar musu da tsaro ga dukiyoyi da rayukansu.