Bom ya kashe sama da mutum 27 a Nasarawa

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga Jihar Nasarawa sun ce aƙalla Fulani 27 ne suka mutu a sakamakon tashin bom da ya auku ranar Talata da daddare a kan iyakar da ta haɗa Nasarawa da Binuwai cikin Ƙaramar Hukumar Doma da ke jihar.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sandan jihar, Ramhan Nansel, shi ne ya tabbatar wa jaridar News Point Nigeria da hakan ranar Laraba.

Ya ce mummunan al’amarin ya faru ne a ƙauyen Rukubi da ke Ƙaramar Hukumar Doma ranar Talata.

Ya ƙara da cewa, rundunar ‘yan sandan jihar tare da takwarorinta na aiki domin gano dalilin aukuwar hakan da kuma tsare duk wani da ke da hannun a ɗayen aikin.

A cewarsa, “Abin takaici ne faruwar hakan. An kashe makiyaya 27 sakamakon tashin bom a yankin Ƙaramar Hukumar Doma.

“‘Yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki tuƙuru don gano dalilin aukuwar hakan da kuma damƙo waɗanda suka aikata hakan.”

Gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya nuna alhininsa kan faruwar hakan, ya sha alwashin kamo ɓatagarin da suka aikata ɗayen aiki don su fuskanci hukunci.