Bom ya tashi a dam ɗin Shiroro a Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fashewar bom da dama sun afku a unguwar Galadiman Kogo, kusa da dam ɗin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa, fashewar ta afku ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Talata.

Ya zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu sakamakon tashin bam ɗin ba, sannan kuma har yanzu ba a kai ga kai ga yankunan da abin ya shafa ba saboda fargabar yiwuwar fashewar wasu abubuwa.

Fashewar na zuwa ne bayan wani tashin bam da ya afku a wannan yankin a shekarar 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *