Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne, ƴan bindinga suka sake dasa waɗansu boma-bomai a babbar hanyar Ɗan-Sadau zuwa Gusau a Jihar Zamfara, waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar matafiya da dama.
Wasu hotunan da kafafen labarai suka wallafa sun nuna yadda mutane suke zube a gefen titi bayan fashewar boma-boman.
Wasu mazauna yankin Ɗan-Sadau sun bayyana wa manema labarai cewa suna zargin ƴan bindiga ne suka dasa boma-boman a titin garin wanda ya haɗe shi da wasu sassan jihar.
Wani mai suna Abdullahi Ɗan-Sadau ya ce wata mota ƙirar Volkswagen Golf 3, ta haye kan wani bom da aka dasa inda a nan take ta tarwatse wanda a sakamakon haka ne mutane shida suka rasa rayukansu yayin da wasu takwas kuma suka samu raunuka.
A lokacin da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’, Kwamandan sojoji na Birget ta ɗaya a jihar, Timothy Opurum ya ce ya umarci dakarun tsaro na atisayen ‘Fansan Yamma’ da su je wajen da abin ya faru don yin nazari a kai.
Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da gidajen jaridu suka fitar a ranar Litinin na cewa yanzu ƴan ta’adda sun fara dasa boma-bomai a matsayin wani sabon salo na gudanar da ayyukansu da suka fito da shi.