Brazil ta tabbatar da Nijeriya a cikin jerin ƙasashen BRICS

Gwamnatin Brazil ta sanar da karɓar Nijeriya a matsayin ƙasa abokiyar haɗin gwiwa a ƙungiyar ƙasashen BRICS. Wannan sanarwa ta fito ne daga ma’aikatar harkokin wajen Brazil a ranar Juma’a.

A cewar Brazil, BRICS da Najeriya suna da muradu iri ɗaya, musamman wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Kudancin duniya da kuma yin kira ga sake fasalin ƙungiyoyin duniya. Brazil ta bayyana cewa Najeriya, wadda ke da yawan jama’a na shida a duniya kuma mafi girma a nahiyar Afirka, na taka muhimmiyar rawa wajen inganta haɗin kan ƙasashe da kuma sake fasalin tsarin shugabancin duniya.

A halin yanzu, Brazil ce ke riƙe da shugabancin BRICS na shekarar 2025, bayan karɓa daga hannun Rasha a ranar 1 ga Janairu. Najeriya ta shiga sahun ƙasashe kamar Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda, da Uzbekistan, a matsayin ƙasa ta tara da aka ƙara a matsayin abokiyar haɗin gwiwa a taron BRICS na 16 da aka gudanar a Kazan, a watan Oktoba na shekarar 2024.