Buƙatar gaggauta farfaɗo da masaƙu da masana’antun Nijeriya

A yau Blueprint Manhaja za ta yi tsokaci ne game da wani muhimmin abu, wanda jama’a da dama ke ganin gwamnatoci da masu hannu da shuni sun yi sake da su har sun lalace ko sun ɓata ɓat. Wannan ba wani abu ba ne illa yadda aka bar masana’antu, masaƙunmu da sauran manyan kamfanoni suka mutu murus, musamman a wannan yanki na Arewacin ƙasar nan, wanda kuma mutuwar waɗannan wurare ba ƙaramin illa ba ne gare mu.

Mun ce ba ƙaramin illa ba ne gare mu bisa la’akari da cewa waɗannan wurare suna sama wa al’ummarmu, musamman matasanmu da dama ayyukan yi, wanda samun waɗannan guraben ayyuka suna matuƙar taimakawa wajen rage munanan ayyuka ga matasa, wanda kuma rashin sa ke jefa da dama daga cikinsu wajen shiga munanan ayyuka.

Waɗannan masaƙu, masana’antu da kamfanoni, a lokacin da suke aiki ba a samun irin fitintinun da ake samu a yanzu, ba a samun yawan ɓata garin da suke da yawa a tsakanin jama’a kamar yada suke a yanzu, ba a samun yawan zauna-gari banza irin waɗanda muke da su a halin yanzu.

Haka kuma a shekarun baya da muke magana a kai, lokacin da waɗannan wurare ke aiki babu yawan al’ummar da muke da ita a yanzu, amma kuma ake da waɗannan wuraren ɗaukar ma’aikata. To idan kuwa haka ne, ai a yanzu ne ma aka fi buƙatar samar da su, bisa la’akari da irin ɗimbin matasan da muke da su, waɗanda wasu ma ko makaranta ba su samu zuwa ba.

Ga duk masu bibiyar abubuwan da ke tafiya na yau da kullum za su iya ganin irin illar da wannan abu ya kawo wa al’umma a wannan zamani. Domin a lokacin da waɗannan wurare ke aiki, abin zai ba ka sha’awa ka ga yadda jama’a ke tururuwa wajen zuwa da kuma dawo aiki, jama’a da dama na cin abinci, baya ga masu ɗaukar albashi, akwai kuma masu jigila da saye da sayarwa a waɗannan wurare. Babu wanda zai iya tantance yawan jama’ar da ke gudanar harkokinsu na samun taro-sisi a irin waɗannan wurare.

A kodayaushe idan aka yi magana game da mutuwar waɗannan wurare, jama’a da dama suna ɗora alhakin abin a kan wiyar gwamnatoci, tun daga na tarayya, jihohi har zuwa Ƙananan Hukumomi na ganin cewa haƙƙinsu ne kula da waɗannan wurare.

Lallai haka ne, Hukumomi ne ke sahun gaba wajen ɗaukar laifi, domin su ne suke da ƙarfin iko da ƙarfin arzikin da za su iya yin huɓɓasa wajen dawo da martabar waɗannan wurare. Amma kuma idan aka yi dogon nazari za a ga cewa ba gwamnati ne kaɗai ke da wannan alhaki, su ma masu hannu da shuni za su shigo ciki.

Wannan ma ya sa masu neman muqamai a waɗannan matakan mulki idan suna neman a zaɓe su, su kan yi alƙawuran cewa za su dawo da martabar waɗannan wurare muddin aka zaɓe su, amma abin takaicin, har yanzu babu wani zaɓaɓɓen da aka yi na ganin hakan, musamman mu dai a nan Arewa.

Kullum idan ana magana kan irin waɗannan masaƙu da kamfanoni da suka ruguje, babu inda takaici zai kama mutum sai in ya yi waiwaye zuwa Kaduna da Kano, inda a wancan lokacin duk waɗannan garuruwa akwai Unguwanni, musamman da iri waɗannan masaƙu ne suka ja masu suna. Misali a Kaduna a ce Kakuri/Maƙera. A Kano kam wuraren suna da yawa.

Wani abin dubawa, lallai kam za a iya cewa duk waɗannan abubuwa laifin gwamnatoci ne, amma ba su kaɗai ba, masu kuɗinmu ma suna da babban laifi. Domin ai ko a masaƙu da kamfanonin da muka yi magana waɗanda suka durƙushe, yawanci na ’yan kasuwa ne, ba gwamnatoci ne kaɗai ke da su ba, me zai hana su ma su sake zuba jari don farfaɗo da su?

Akwai wani lokaci ina wucewa ta jikin ɗaya daga cikin waɗannan masaƙu, masaƙar sarrafa auduga ta KTL, inda na ga yara ne ke ƙwallo a ƙofar shiga masaƙar. Wannan abu sai da ya nemi ya sanya ni zubar da hawaye.

Domin ana yawan maganar cewa ba za a iya bar wa gwamnatin komai a ce sai ita ce za ta yi ba, musamman a wannan zamani da muke da yawan da ya wuce misali, musamman a tsakanin matasa. Domin a halin yanzu an ce a Nijeriya muna kusan mutum Miliyan 200 ne. Don haka lallai wajibi ne masu kuɗinmu su shigo ciki don ceto matasan nan namu daga halin da suke ciki na rashin aikin yi.

Rashin tsaron da muke fama da shi yanzu a ƙasar nan, musamman a nan Arewa yana tsoratar da masu zuba jari daga ƙasashen wajen su zo don kafa masana’antu, har ma da namu masu kuɗin, duk da yake wasu Gwamnoni suna ƙoƙarin wayar da kan irin waɗannan ’yan ƙasashen wajen cewa abin bai kai yadda suke gani a kafafen yaɗa labarai ba, inda kuma wasu ke zuwa suna dubawa. Musamman a Kaduna, Malam Nasiru El-rufai yana ƙoƙarin gudanar da waɗannan abubuwa.

To, amma duk da haka, ina ganin ai sai mu ’yan ƙasa mun yi wani huɓɓasa, gwamnatocinmu da masu kuɗinmu mun kafa irin waɗannan masana’antu, sannan su waɗannan ’yan ƙasashen wajen sun ga alama da gaske ne kafin har su ma su saki jiki su zo su kafa.

Manhaja na ganin cewa akwai gayar muhimmancin a farfaɗo da irin waɗannan masana’antu bisa la’akari da cewa mutuwarsu ne ummul haba’isin kusan duk fitintinu da rugingimun da suke addabarmu a wannan yanki namu da ƙasar baki ɗaya.

Shi matashi, idan yau ya wayi gari ya ga akwai inda zai je ya samu taro-sisi, musamman waɗanda ba sa zuwa makaranta, to ba yadda za a yi a yi amfani da shi wajen aikata wani mummunan abu. Amma idan aka wayi yau matashi ba inda zai je, to zai iya shiga kowane irin hali don samun abin da zai biya buƙata, ko da kuwa ta mummunar hanya ce.

Wannan ne ya sa muke da tunanin cewa rugujewar waɗannan masana’antu da kamfanoni ya taimaka matuƙa wajen jefa ƙasar nan cikin mummunan halin da ta ke ciki na rashin tsaro, bisa la’akari da yawan matasan da ba su da inda za su je don neman abin da za su ci.

Saboda haka yana da matuƙar muhimmanci ga gwamnatoci da masu hannu da shuni su zo su sake duba batun farfaɗo da waɗannan wurare don amfanin al’ummarsu, su samu riba, sannan kuma jama’a su samu aikin yi da zai taimaka masu wajen magance matsalolin su na yau da kullum.