Buƙatar tsaftace babban titin Abuja zuwa Kaduna

Kiran da Majalisar Wakilai ta yi na cewa, shugaban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, da Sufeto Janar na ’yan sanda, Usman Baba, ya kamata su magance yawaitar hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kan matafiya a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da sauran hanyoyin ƙasar nan, duk da cewa an makara, ya dace kuma abin a yaba ne.

Majalisar ta kuma umurci dukkanin kwamitocin ta kan harkokin tsaro da su riqa tattaunawa da hukumomin tsaro duk wata tare da bayyana wa shugabanni da ɗaukacin zauren majalisar a kowane wata da kuma wata uku kan abubuwan da hukumomin ke yi na magance matsalolin tsaro.

Wani ɗan majalisar, Mohammed Nalaraba, ya gabatar da ƙudiri na gaggawa ga jama’a a zauren majalisar a ranar Laraba domin kokawa kan hare-haren da aka kai kan hanyar Kaduna da babban birnin ƙasar.

Nalaraba ya ce, an samu rahoton jami’an tsaro cewa, ’yan bindiga na sake haɗuwa a ƙauyen Rijana da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Ya kuma ce duk da bayanan sirri da aka samu, babu wani abu da jami’an tsaro suka yi domin fatattakarsu, kuma ‘yan ta’addan a yanzu suna gudanar da ayyukansu daga sabbin maɓoyarsu ba tare da an hana su ba.

Ɗan majalisar wanda ya tambayi dalilin da ya sa har yanzu jami’an tsaro ba su bi sahun masu laifin ba, ya ce, “Rijana ba kamar dajin Zamfara ba ne, ƙaramar al’umma ce kuma waɗannan ‘yan bindiga sun sake haɗuwa a can, kuma idan ba a kula ba, nan ba da daɗewa ba za su wuce Suleja sannan su shiga Abuja.”

Nalaraba ya bayyana damuwarsa kan tashe-tashen hankulan da ake fama da su na tsaro a faɗin ƙasar, wanda a cewarsa, ya janyo asarar rayuka da dama, ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Ya ce, ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare kan matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suke kashewa tare da yin garkuwa da ‘yan Nijeriya ba tare da hukunta su ba.

Ɗan majalisar ya koka kan yadda hanyoyin Nijeriya musamman hanyar Kaduna zuwa Abuja da ke ɗaya daga cikin mafi yawan jama’a a ƙasar nan ba su da tsaro, musamman a ƙarshen mako, inda ya ce, lamarin ya yi muni ta yadda hatta manyan jami’an sojoji da jami’an tsaro da masu rakiya ba za su iya bi ba.

“Muna aiki a kan kasafin kuɗin 2022 kuma ina sane da cewa maƙudan kuɗaɗe a kasafin kuɗin na zuwa ne a fannin tsaro, ko da ‘yan Nijeriya na mutuwa,” inji shi.

Nalaraba ya bayyana cewa, majalisar a matsayinta na wakilan jama’a, kamata ya yi ta umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakin fatattakar ‘yan bindiga daga maɓoyarsu da kuma tabbatar da hanyoyin da ’yan Nijeriya za su iya tafiya.

“Hanyar Abuja zuwa Kaduna na ɗaya daga cikin manyan titunan ƙasar nan. Ita ce hanyar da manomanmu na Arewa suke amfani da su wajen kai amfanin gonarsu zuwa kasuwa a Kudu. Idan ba za mu iya zuwa Kaduna ko wasu sassan Arewa ba, to me ya sa muke cikin Majalisar Tarayya?”

A nasa gudunmuwar, Nicholas Ossai ya kuma yi Allah wadai da cewa hare-haren da ake kai wa kan tituna a halin yanzu ya zama ruwan dare duk da ɗimbin kason da ake bai wa tsaro.

Hakazalika, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro da su ƙara sanya ido a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare, inda ‘yan bindiga ke sacewa ko kashe matafiya da ke kan hanyar.

Haƙiƙa abin takaici ne yadda matsalar tsaro a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama mai muni da ban tsoro ta yadda har jiga-jigan siyasa a halin yanzu suna cikin haɗari. Wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun harbe wani babban ɗan siyasa kuma ɗan takarar gwamna a zaɓen 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara, Sagir Hamidu Gusau, a ƙauyen Rijana da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, da yammacin Lahadi.

An ce, jami’an tsaro sun kai gawar marigayi Gusau asibitin da ba a san ko su waye ba a Kaduna kafin daga bisani su miƙa gawarsa ga iyalansa da safiyar Litinin domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ayyukan jiragen ƙasa da ake kallonsu a matsayin wani zaɓi na yawaitar munanan laifuka a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ta hanyar fasinjoji da suka haɗa da ‘yan siyasa da sauran masu faɗa a ji a cikin al’umma, shi ma ba a bar su a baya ba, saboda a kwanan baya an kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya NRC ta tabbatar da cewa, wasu da ake zargin ‘yan bindiga da maƙare ne sun lalata wani yanki na hanyar dogo daga Abuja zuwa Kaduna da bama-bamai, lamarin da ya sa aka daƙile ayyukan jiragen ƙasa a kan hanyar.

Manajan Daraktan NRC, Fidet Okhiria, ya ce, abubuwan fashewar sun lalata hanyar jirgin ƙasa a wani wuri da ke tsakanin Dutse da Rijana, yankin da ya fuskanci hare-haren ‘yan bindiga da dama a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Tun da farko, wani tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayar da rahoto a shafinsa na Facebook cewa, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Ya ce, ‘yan bindigar sun tayar da bama-baman da ya lalata titin jirgin tare da farfasa gilashin injin jirgin da yammacin Laraba.

Sani ya ce, ‘yan bindigar sun kuma buɗe wuta kan jirgin a safiyar ranar Alhamis, inda suka auka wa direban da tankin jirgin. Abin ya faru ne a tsakanin tashoshin Dutse da Rijana. Direban ya yi ta fama ya nufi tashar Kaduna Rigasa.

“Da sanyin safiyar nan, ina cikin jirgin ne jirgin mu ya ci karo da wani bam da ya lalata layin dogo. Jirgin ya kusa zarce daga kan hanyarsa, sannan muka kuɓuta ta hanyar mu’ujiza,” Shehu Sani ya rubuta.

Wani abin takaici shi ne yadda wata babbar hanya ta kasa kamar babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna za ta iya kutsawa cikin gaggarumin kutsawa daga miyagu da ga dukkan alamu jami’an tsaro ba su da taimako. Wannan ba abin yarda ba ne kuma dole ne a magance shi nan take.

Don haka muna kira ga Majalisar Wakilai da ta wuce ɗaukaka ƙara ta hanyar zartar da ƙudiri na tilastawa jami’an tsaro ɗaukar kwakkwaran mataki wajen tabbatar da tsaron babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.