Buɗɗaɗiyar wasiƙa zuwa ga Yasir Ramadan Gwale

Gaskiya na karanta jawabin da aka yi ta ranar juma’a 29 ga watan Yuli zuwa huɗu ga watan Agustan 2022. Haƙiƙa ka bayyana gaskiya ba tare da inda-inda ba, sai dai nace Allah Ya ƙara basira.

Bayan haka ina so na yi tsokaci kaɗan, amma kuma zan zurfafa bisa ga yadda al’amarin ya ke wakana kafin ababen su caɓe su kasance cikin mummunar makoma wacce ta addabi duk ɗan Nijeriya ko a gida ko wajen Nijeriya. A yau gaskiya ne shugaba Buhari yasha faɗin yaɗa abubuwa suka rincaɓe a wancan lokutan shugabannin baya kuma ai gaskiyane ba daga 2015 bane ababen suka kasance idan dai za’a dubi abubuwan da idon rahama, kususan mu a Arewa babban abinda yafi ci mana tuwo a ƙwarya shi ne 2007 zuwa 2019 kususan ɓullowar Boko Haram.

Sannan sai satar shanu ta kunno kai, waɗannan sune sukafi shahara, amma dai sauran ababen tuni ake aikatasu a kudu maso gabas, da kudu maso kudu, kar harda kudu maso yamma!

Ashe dai mafarin waɗannan alkaba’ai sun faru kawai bayan yaƙin basasa na Nijeriya wato daga shekarar 1967 – 1970; kuma duk lokutan mulkin soja, an sami abubuwan ta’adda, kamar ta’addancin ‘yan fashi da makami, masu yunƙurin fita daga Nijeriya, masu fasa bututun mai fetur da makamantansu; waɗannan haƙiƙa an daɗe da samunsu, kuma suka riƙa har suke samun ƙarfin daya wuce misali, wanda har yake neman fin ƙarfin gwamnati.

Haƙiƙa shi shugaba Buhari soja ne, kuma yana ganin mulkin farar hula kamar na soja ne, wanda duk ababen da ya ce ayi haka za a yi, koda yake koda mulkin soja da ya yi waɗanda suka assasa fitarsa daga mulkin a shekarar 1985, sunce wai baya jin shawara, su kuma suka zo suka shara aguje bayan wani yaci zaɓe sun soke, kuma ‘yan kudu maso yamma suka yi mummunan cari wanda suka ba da mulki suka tsere.

Gaskiyar lamari shine shugaba Buhari ya shigo da niyyar ganin komai ya daidaita ga wataƙil talaka, amma bai yi la’akari da yadda mulkin soji ya sha bam-bam dana farar hula ba: shugaba Buhari yasan cewa shugabannin soji da suka yi mulki akwai waɗanda suka yi babakere da rufda ciki akan dukiyar Nijeriya fiye da kima, kuma gaskiya sun shahara wurin yin wannan katoɓara; sannan mulki ya koma ga farar hula a shekarar 1999; wanda sojoji suka bada mulkin ga ɗaya daga cikinsu, shine Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya, daga 1999 – 2007; kuma anga abubuwan da suka faru cikin shekaru takwas; 2007 – 2011; farar hula sun karɓi mulki tsakanin marigayi Umaru Musa Yar’adua bawan Allah mai son jama’a, mawadacin zuci, ba mai son wawason kuɗin gwamnati ba, yayi irin nasa mulki domin ceto Nijeriya, amma aka sako masa karan tsana har Allah Ta’ala Ya karɓi ran bawansa kuma anga yadda yaso ya gyara Nijeriya da sakata a kyakkyawar hanyar arziƙi, amma ‘yan gaza gani suka ƙuntata masa kuma yar yanzu muna cikin masifar lalacewar mulki a Nijeriya.

Bayan marigayi Umaru Musa Yar’adua sai shi Mr. Jonathan wanda ya gaji marigayi Yar’adua, Allah Ya sashi a Aljannah Firdausi, Amin Summa Amin. To sho Jonathan ya yi mulki irin nasa babu yabo babu fallasa; domin shima saida ya hau gadon ƙaya domin yaƙi yarda a juya shi kamar waina cikin tanda. To kaga mulkin Jonathan zuwa 2015, APC ta karbi mulki ƙarƙashin farin jinin Shugaba Buhari.

Buhari ya sami farin jini ne lokacin da ya hau mulki a 2984 zuwa Agusta 1985. Cikin lokacin ya kawo irin ra’ayin Janar Murtala Ramat Muhammad na kawo sauƙin komi ga talaka; anga yadda aka rinƙa sayar da kayan masarufi cikin sauƙi da yadda aka aiwatar da wata doka wai “War against Indiscipline (WAI)”.

Duk da niyyarsa kowa yabi doka da dai sauran abubuwa, domin gyara ƙasa. To malam kaga farkon ababen da suka shigo da farin jinin shugaba Buhari a zuciyoyin jama’a kususan talakawa.

An yi masa juyin mulki kuma sa’a ta ƙara bayyana a gunsa a shekarar 2015 ya sake zama shugaban ƙasa bayan shan kaye da ya yi ta samu tun a shekarun 2003, 2007, 2011, 2019 – sai a 2015 ya samu damar ɗarewa a kan mulkin ƙasa Nijeriya.

Kaga shi shugaba Buhari niyyarsa ya saita Nijeriya, amma niyyarsa ta binciken shugabannin baya, sai ya zame masa wuƙa a maƙogwaro, kuma ya jawo masa maƙiya na fili dana voye, wanda alal haƙiƙa suke da komai a hannunsu wanda koda acan Amurka akwai irinsu sai yadda suke so za a yi inba haka ba, sa ga yadda buƙata za ta yalwata ga ƙasa.

Duk yadda shugaba yake so haka za a yi, dubi dai ta yadda marigayi Sani Abacha shi kaɗai a wuri ɗaya ya bawa Bayelsa jiha, kuma ta bayu domin tsananin mulki irin na soja, kaga ai yankin Neja-Delta ne; gwamnati NPC wacce take ta Arewa ce, ita ce ta ƙirƙiro wurin, yau da suka zama jihohi huɗu suma sukan yiwa shugabannin Arewa mummunar suka, kamar yadda sauran jihohin kudu suke yi, kususan ƙasar Inyamurai (Igbo).

Kodayake wataƙila naso na canza dalilin wannan wasiƙa ga malami na, amma dai tuna baya, kususan alkhairi abu ne mai kyau ƙwarai da gaske. su waɗannan alkaba’ai da suka cikuikuye wannan ƙasa abune kamar gado kuma wataƙil takun da jami’an tsaro suke yi suna duba yadda duniya za ta kalle su wataƙil shi ya sa yaqin ya ɗauki lokaci mai tsawon gaske. Ai kaga yaƙin basasa shekaru uku aka yi kacal 1967 – 1979, amma wannan an sami kusan shekaru barkatai; domin tun 2009 aka fara da ‘yan Boko Haram, amma duk da cewa akwai ‘yan OPC daga Yoruba, ‘Yan Biafra daga kudu ta gabashin Nijeriya.

Shugaba Buhari yayi rawar gani na mayar da Nijeriya ƙasa haka, ya sassauko da kayan masarufi a shekarar 1984-1985; shi ne farin jinin shugaba Buhari daga jama’ar Nijeriya ya maimaitu, domin a gane cewa zamantowarsa shugaban farar hula abin ya sha bam-bam, wannan koda maƙiyin shugaba Buhari yasan da haka, amma shekarun nan bakwai jama’a mun shiga cikin mawuyacin hali, domin wallahi talakawa irina mukan bar gidajenmu ko kukar kaɗa miya babu, balle masarar da za’a tuƙa tuwo, to ga kuma masifar ‘yan fashi da sauransu, mu kwana nan.

Daga naku Kwamared Ibrahim Abdu Zango
Chairman: Kano Unity Forum, Kano – Nigeria, 08175472298.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *