Daga MUSBAHU BAFFA NA ‘YAR TALLA (Bakwankwashe)
Bayan gausuwa mai tarin yawa da fatan kana cikin ƙoshin lafiya. Tabbas zuwanka a matsayin Gwabnan Jahar Kano a irin wannan yanayin da Jahar ta samu kanta ba ƙaramar nasara ba ce ga al’ummar Jahar.
Ka zo a gaɓar da aka cefanar da asibitin Yara na Hasiya Bayero akan kuɗi Naira Miliyan 6 kacal, duk kuwa da irin yadda al’ummar Jahar ke amfanuwa da shi.
Ka zo a gavar da aka rushe Kotu guda ba tare da sanin Alƙalin Kotun ba, aka cefanar da gurin don gina Plaza.
Ka zo a gaɓar da aka cefanar wa da ɗan Lele ma’aikata sukutum da guda, inda aka bai wa cikakkun ma’aikatan Gwabnati notice ɗin fita.
Ka zo a gaɓar da aka kwashe manya manyan injinan hasken wutar lantarkin asibitin Nassarawa a kan kuɗi Naira Miliyan 60, duk kuwa da cewa darajarsu ta haura Naira Miliyan 800. Ba a kuma damu da majinyata da ke kwance a asibitin ba.
Ka zo a gaɓar da birnin Kano da kewaye suke cikin matuƙar jin ƙishi sakamakon rashin ruwan famfo da ya addabi al’umma.
Ka zo a gaɓar da birnin Kano ya vaci da ɓata garin yara da suke kashe rayukan mutane masu amfani a cikin al’umma a kan wayar hannu da ba lallai ta haura dubu 100 ba.
Ka zo a gaɓar da al’ummar Kano ke kokawa kan rufe makarantun kwana na ‘yan Mata ba tare da an nuna damuwa da amfanin su cikin al’umma ba.
Ka zo a gaɓar da al’ummar Kano ke kokawa kan makomar ilimin yaransu sakamakon rushe aji don buƙatar wani ta son ƙarin filin makarantar da aka cefanar masa.
Ka zo a gaɓar da al’ummar Kano ke kokawa kan makomar makarantar Management da aka cefanar da ragowar ɗan filin da ya rage a cikin ta.
Mai girma Gwabna, idan na tsaya zayyano irin abubuwan da ka zo ka tarar wadanda ke buqatar neman agajinka ina kyautata zaton zan kwana ban kammala ba.
Mai girma Gwabna, mun shaida ire-iren matakin da ka yi alƙawarin ɗauka a kan gine-ginen da wasu shafaffu da mai suka yi a filayen Gwabnati, wadanda al’umma ke amfanar su ta mabambantan hanyoyi.
Tabbas mai girma Gwabna duk masoyin Jahar Kano zai yi farin ciki da irin yadda ka ɗauko hanyar saitagarin, musamman ta fuskar muhalli.
Sai dai mai girma Gwabna, ina neman alfarma ɗaya a matsayina na masoyinka, kuma wanda ya bayar da ƙwaƙƙwarar gudummawar samun nasararka.
Mai girma Gwabna, fiye da kaso casa’in na mutanen da ke Kasuwanci a manyan shagunan da ka ziyarta, ko kake neman ziyarta ba mallakinsu ba ne, zaman haya suke. Kenan rushe wajen ba asarar su ba ce, domin kuwa idan ma suna da asara bai wuce ta rasa gurin sana’ar da suka saba da shi ba.
Don haka, Ya Mai girma Gwabna, me zai hana dan a kiyaye alfarmar dukiyar ire-iren wadannan mutanen a ringa ba su notice na su kwashe kayansu a tsanake, ta yadda ba za su yi asara ba?
Domin a halin da ake ciki yanzu Ya Mai girma Gwabna, vata gari suna neman karve ragamar aikin da ka faro shi bisa niyyar saita birnin Kano. Inda suke riga Malam masallaci suna vallewa mutane shaguna suna yi musu sata.
Kuma yana da kyau a samar da cikakken tsaro a yayin da duk aka wanzar da irin wannan aikin alkhairin domin guje wa ɓallewar doka da oda.
Sannan mai girma Gwabna, yana da kyau duk inda ya kasance za a rushe ya zamanto sananne ga mazauna wannan wajen domin fita haƙƙinsu. Su dai ‘yan zaman haya ne, ba mamallaka ba. Don haka babu komai idan an sanar da su.
Ya Mai girma Gwabna, asara ba ta da daɗi ko kaɗan. Musamman ga mutanen da suka san cewa ba ta hanyar harƙalla suka mallaki dukiyarsu ba.
Ya Mai girma Gwabna a taimaka a duba wannan ƙorafin nawa.
Musbahu Baffa, Bakwankwashe ne na gidi, kuma masoyin Jahar Kano da al’ummar Jahar Kano.