Buɗe ƙofar fahimtar juna tsakanin ma’aurata (2)

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa, sannunku da jimirin karatun Manhajarku mai farinjini.

A wannan karon ma muna tafe ne da ci gaba a kan mas’alar da muke tattaunawa a makon da ya gabata. Wato yadda ma’aurata za su samar wa kansu yanayi mai kyau na fahimtar juna da zai samar musu da zaman lafiya mai ɗorewa. A mako da ya gabata mun kawo wasu alamomi da suke nuna aurenku yana cikin gararin rashin fahimta. Sannan kuma mun kawo muku hanyoyin da za a shawo kan rashin fahimtar inda muka kawo hanyoyi guda tara. Yanzu za mu ɗora insha’Allah. A sha karatu lafiya:

  1. Yafe kuskuren baya: Idan matsala ta faru tsakanin ma’aurata a daina tuna kuskuren baya. Yin haka ba ƙaramin cakuɗa matsala yake ba. Duk irin ciwon da laifin baya ya yi muku, ku yi haƙuri ku yafi juna. Ku ma kuna son watarana a yafe muku. Don ba kullum ake kwana gado ba. Wataran ku ma za ku iya saɓa wa wani ku ji kuna son a yafe muku. Yafiyar tana qara muku kusanci da kuma fahimtar juna da zaman lafiya. 
  2. Magana cikin tsanaki yayin rashin fahimta: Idan rashin fahimta ya faru tsakanin ma’aurata yana da kyau a zauna a yi magana ba wai husuma ba. Ɗaga wa juna murya da nuna wa juna yatsa ba zai ba da taimako wajen kawo fahimta ba sai ma ya sa matsalar ta ƙara taɓarɓarewa. Sannan yana ƙara zafafa muhawarar da kuke yi. A wajen namiji kuwa, in dai zai yarda su dinga yin wannan sa’insa da matarsa, wallahi raini ya riga ya shiga. Da wuya ƙimarsa ta iya dawowa a idonta. Kuma tun tana shiru fa watarana za ta rama. Shi ya sa ma fi a’ala, Yayana daga ka ga rashin fahimtar zai zama faɗa tsakaninka da ita, haɗiye ji-ji da kanka na namiji da ganin kai ne a sama. Ka fice ka bar mata gidan/ɗakin.

Wallahi idan ka yi haka za ka gode min. Ita kanta nadama za ta kama ta in dai mai kunyar ce kuma tana sonka tsakani da Allah. Ke kuma ‘yar’uwa ki sani, ɗaga masa murya haramun ne kuma Allah yana fushi da mai kyarar mijinta. Kuma ƙimarki tana zubewa wajensa. Sannan a irin haka za ki tunzura shi ya sake ki ko ya yi miki duka. Daga ƙarshe ku yi ta nadama dukkanku. 

  1. Kunyata munafukai: Daga zarar da kuka ƙulla alaƙa ta aure ku sani, kun shata layin yaƙi tsakaninku da munafukai, mahassada, da maƙiya har ma da shaiɗanun mutane da aljanu. Don haka ba komai za a faɗa muku a kan juna ku ɗauka ba. Idan kuka ji wai abu gara ku tunkari juna don tabbatarwa. Kada ku bar abin a ranku ya dame ku har ya haifar muku da zargi da saɓani a zaman aurenku. Idan da hali ma ku kira munafukin ku titsiye shi ko ita ba zai ƙara ba. Ko da kuwa na jiki ne. Haka shi ne samun fahimta da zaman lafiyarku. 
  2. Banda ya da wa juna magana da sunan wasa: Masu magana dai sun ce wai wasan Bahaushe, gaskiyarsa. Akwai mutanen da sukan huce haushin juna ta hanyar raha. Sai a gaya wa juna baƙar magana cikin wasa da dariya. Hakan yana kawo ƙullatar juna da ta’azzara rashin fahimta da zaman lafiya. Gara a yi wasa mara illa wanda ba zai zama cin fuska ko ya tava mutuncin juna ba. 
  3. Nuna rashin girmamawa: Idan saɓani ya shiga tsakanin ma’aurata, ɗaya ya so ya yi bayani a ba shi dama. Kada a yi banza da shi a cigaba da wasu abubuwan kamar danna waya ko kallon talabijin ko wani abu. Hakan rashin girmamawa ce ƙarara. Kuma zai ƙullaci haka. Idan miji ne ya yi wa mata hakan, za ta bari sai shi ma yana son magana da ita ma sai ta ce za ta rama don shi ma ya ji yadda ta ji. Ka ga an ƙara samun rashin fahimta a tsakanin juna. Haka za a yi ta zama a rashin daɗi. Don rashin fahimtar juna tana sa zaman daɗi ya yi ƙaura. Ba da cikakken kulawa a yaiyn magana ko ma wasa abokin zama yake a zaman aure kada a share shi, gaskiya yana da matuƙar muhimmanci a aure. 
  4. Banda katse juna a magana: A lokacin da aka samu rashin fahimta tsakanin ma’aurata sai miji ko mata suka zo da ƙorafinsu ga juna ya kamata wanda ake gaya wa ya tsaya ya saurara ba tare da an katse wanda yake maganar ba. Yin hakan girmamawa ce kuma ita ce kaɗai hanyar da za a fahimci juna har a yi gyara. Katse mutum ko ba miji ko matarka ba ne gaskiya ba abinda ya ke kawowa sai zazzafar muhawara da cacar baki. Don haka ku saurari abokan zamanku yayin da suke gabatar da ƙorafinsu. Ku ma sai ku dinga kafa naku hujjojin a zuciya amma. Sai ka daure fa amma. Musamman idan abinda suke faɗa ƙorafi ne a kan kuskuren abinda ba ka yi ba. Idan sun kai aya, sai shi ma ɗayan a bar shi/ta ya yi bayani ba tare da an katse shi ba. Hakan shi ne adalci kuma shi ne hanyar maslaha. Kuma kamar yadda na faɗa tun a kashi na ɗaya, dole idan an zo tattaunawar da ma fa a kai zuciya nesa. Kuma a sa ran ana ƙoƙarin warware matsala ne ba wai muhawara ake yi wacce ɗaya zai samu nasara a kan ɗaya ba. Ku samu fahimtar juna ita ce babbar nasararku. 
  5. Zaɓen muhallin tattaunawa: Na san mai karatu zai ce meye alaƙar muhalli da fahimtar juna? Amma muhalli yana da tasiri ƙwarai da gaske. A zaɓi muhalli da yanayin da ya dace a tattauna. 
  6. Tattaunawa gaba da gaba: Ya kamata ma’aurata idan suna da matsala da juna, su tattauna gaba da gaba ba wai su ce za su wakilta wani ba ko kuma su ce za su turo da saƙon waya ko wasiƙa. Yin haka tamkar mai yin ciwo daban wanda ake ba wa magani daban. Don haka kai ka san matarka ka san yadda za ka ɓullo ta fahimce ka. Ke ma haka, ba zancen tsoro. Ki tunkare shi kawai. Tun ba ya fahimta wataran zai fahimta. Gaya wa wani ba zai warware matsalarku ba. Amma fa kamar yadda na faɗa a baya, yayin tattaunawar a zaɓi muhalli da yanayi da lokaci yana da muhimmanci. Domin idan ba a saita yanayi ba, za a samu akasin abinda ake buƙata. Sannan a tattara dukkan tunani a tattaunawar. Hakan zai nuna wa abokin zama irin girmamawa da muhimmancinsa a gare ki. 
  7. Faɗar gaskiya ga aboki/abokiyar zama: Kamar yadda Hausawa kan ce wai gaskiya ɗaci gare ta. Amma ita ɗin jigo ce wajen samar da fahimtar juna tsakanin ma’aurata. Faɗa wa juna gaskiya a dukkan lamurra yana kawo fahimtar juna, cire zargi har ma da ƙara haɓaka amana a tsakanin juna. Gaskiya an san tana da ɗaci amma a juri faɗarta ya fi zaman ƙarya da juna. Kuma ko gurin Allah ka fita. Idan mata ko miji ne suka san su ne da laifi kawai su daure su faɗi cewa su ne, kuma su ba da haƙuri. Maimakon mutum ya yi ta musu da ƙoƙarin kare laifin da ya riga ya san ya aikata. An san dai akwai lokacin da faɗar gaskiyar zai iya zama fitina. Kamar namiji ya je zance wajen wata ya ce wa matar ai gidan abokinsa ya je, saboda gudun husuma. Amma ƙarya idan ta yi yawa, tana ruguza kowacce irin alaƙa. 
  8. Jan juna a jiki: Yayin da ake tattauna wata matsala idan an samu savani yana da kyau a zauna kusa da juna. Idan so samu ne ma a kai hannu a shafi ko a dinga taɓa juna. Hakan yana matuƙar ƙara sakko da fushi da kuma haɗin kai da ƙara fahimtar juna. 
  9. Yin raha da juna: Yana da kyau idan za a tattauna kan wata matsala ko saɓani a yi cikin raha da nishaɗi. Musamman idan za a yi wa mutum gyara a kan wani abu. Yayana tunda ba ‘yarka ba ce ka tausasa kalamai ga matarka. Za ta ji ka girmama ta, ita ma za ta ga girma da qimarka. Yi mata tsawa da cin mutunci idan ta yi kuskure ba zai kawo maslaha ba. Wata ma ba za ta fahimci meye laifin da ake so ta gyara ba. Kawai abinda za ta hango, so kake ka ci mutuncinta. Kuma sai ta ƙudurta a zuciyarta sai ta rama abinda ka yi mata. Ko da cikin dabara ne. Ka tuna lokacin da kake zuwa zance wajenta kafin ta zama matarka. Idan ta yi laifi haka kake mata? Ke ma ‘yaruwa idan za ki gyara wa mijinki wani abu a zaman aurenku, ki gaya masa cikin hikima da lallashi. Idan so samu ne ma, a cikin wasa da dariya. 

To bayan waɗannan matakan ya kamata kuma ma’aurata su sani, ba wai rigima ce ba a yi a gidan aure ba. Amma yadda kuka ɓullo wa wannan saɓanin shi yake sa wa zaman aure ku ya ƙara ƙarko ko kuma ya ruguje. Saɓani yana ƙara fahimtar juna da kusanci in dai har an bi hanyar warware shi cikin maslaha. 

Kuma buɗe ƙofar fahimta tsakaninku ita ce mabuɗin samun zaman lafiya da rayuwar aure mai ɗorewa. Amma fa ba a ce yana da sauƙi ba. Dole sai kun yi uzuri da haƙuri da jajircewa da kawar da kai sannan za ku girbi ganimar zaman lafiya da fahimtar juna a zaman aure. Don haka, sai a hankali. Don wasu ma’auratan ma kan shafe shekaru kafin su kai ga hakan. 

Idan kuma ma’auratan suka kasa shawo lamarinsu, za su iya neman shawara wajen masana ko kuma wasu mutane amintattu a wajensu. 

A nan zan dasa aya. Mu haɗu a wani makon. Ina jinjina ga makarantana da suke kirana koyaushe don yi min addu’a ko tsokaci ko ba ni shawara. Na gode ƙwarai Allah ya biya ku. Mu haɗu a wani makon.