Buɗe kakar siyasa, lokacin yaudarar talakawa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun kafin ’yan Nijeriya su shiga wannan shekara ta 2022 aka fara ganin alamun yadda ’yan siyasa ke zumuɗin ganin shekarar 2021 ta wuce da sauri, don su fara hidimar da suka fi so kuma suka fi iyawa, wato shiga takarar neman kujerun mulki, yaƙin neman zaɓe, shiga ƙauyuka da fitar da kuɗaɗe don gudanar da wasu ayyuka na taimakon jama’a, duk dai da nufin jan hankalin talakawa, domin su amince su zaɓe su.

Duk wata jiha da ka shiga za ka ga hotunan ’yan takara mammanne a tituna, gidajen jama’a har da gine-ginen gwamnati, duk kuwa da yake hukumar zaɓe ta INEC ba ta fitar da da jadawalin fara harkokin siyasa ba, amma da yake waɗannan ’yan siyasa sun saba da riga malam masallaci, suna son komai a fara da zafi-zafi, musamman ga sabbin ’yan takara.

Wannan ce shekarar da kakar ’yan siyasa ke buɗewa ka’in-da-na’in, inda za ka riqa jin canjin sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Jam’iyyun siyasa za su riqa zawarcin ’yan takara, domin neman magoya baya. Yayin da za ka yi ta samun rahotannin shirya tarukan jam’iyyu don fitar da deliget da za su sa ido wajen zaɓukan fitar da gwani, inda ake camamar cinikin ɗan takarar da ya fi ba da kuɗi da kyautatawa, masu fitar da ’yan takara.

Tuni wasu har sun fara jin ƙamshin romon dimukuraɗiyya, wasu ma har sun fara ɗanɗanawa. Domin kuwa, a wasu wuraren kamar a Jihar Kano, an ga yadda sabbin ’yan takarar kujerar Gwamnan jihar ke rige-rigen raba kuɗaɗe da ba da tallafin karatu da na sana’o’in dogaro da kai, domin jan hankalin jama’a.

Matasa ’yan Soshiyal Midiya da ke bibiyar ’yan siyasa suna musu yaƙin neman zaɓe ta zaurukan sada zumunta, su ma sun fara jan nasu kason. Zaurukan sada zumunta sun fara ɗaukar zafi, ɓangarorin matasa daban-daban suna ta yi wa juna yarfe da jefa maganganu na suka ko kushe ɗan takarar wani ɓangare.

Su ma kansu ’yan jarida yanzu ne kakar samun kuɗin su daga wajen ’yan siyasa, waɗanda ke mantawa da su ko daina ɗaukar wayoyin su bayan zaɓe, idan buƙatar ta biya. Kafafen yaɗa labarai sun samu abin faɗa, wajen shirya tattaunawa da  muhawara a tsakanin manyan ’yan siyasa da ake ganin suna da ra’ayin shiga takara da zarar Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta bayar da dama, ko da yake wasu tuni fostocin su sun cika gari.

Ba da jimawa ba, shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Ahmad Bola Tinubu da tsohon Gwamnan Jihar Abiya kuma Sanata a Majalisar Ƙasa, David Umahi, Ministan Sufuri Rochas Okorocha, da ɗan kasuwa.

Dr Ibrahim Bello Dauda, da suka bayyana aniyarsu ta shiga neman takarar shugabancin Nijeriya a babban zaɓen 2023 a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC. Har ma wasu daga cikin su suka je takanas har fadar shugaban ƙasa, su sanar ka da shi, domin neman goyon bayan sa.

Yayin da a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP akwai irin su tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan wanda ake ta raɗe-raɗin dawo wa fagen siyasa, ga kuma tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP Ahmad Mu’azu, da sauran ’yan siyasar da ke dakon jiran lokaci da ya dace su bayyana buƙatar takarar su, ko da yake wasu tuni labari ya yaɗu, cewa suna son su su shiga takara, amma sun noƙe suna nazartar yanayin.

Tuni muhawara ta yi nisa a zaurukan sada zumunta da kafafen watsa labarai, inda ake tattaunawa da bayyana ra’ayoyi kan dacewa da cancantar wasu ’yan takara. Ma fi jan hankali shi ne irin yadda matasa ke bayyana ra’ayoyin su game da dacewar a bai wa matasa masu jini a jiki, waɗanda ke da wayewar zamani, damar su fito su nuna tasu ƙwarewar, domin kawo sabbin sauye-sauye da za su kawo wa Nijeriya cigaba mai ma’ana.

Lallai ne a daidai wannan waje mu ja hankalin matasa a kaucewa shiga bangar siyasa, ta ɗaukar makami ko ta cikin Soshiyal Midiya, inda za su riƙa cin mutuncin mutane da razana su ko aibata juna. Ya kamata matasa su fahimci cewa irin wannan halayya ba ta dace da cigaban rayuwa da makomar su ba. A maimakon haka su zama masu kishin kansu da ƙasar su, kada su yi wani abu da zai kawo tashin hankali da rashin tsaro a ƙasa, saboda son zuciyar wani ɗan siyasa. Su shiga makaranta su yi karatu, domin su ma wata rana su zama wani abu a cikin al’umma.

Shawara ta ga ’yan uwana talakawa duk wata dama da suka samu a wannan lokaci su yi amfani da ita. Duk wani ɗan siyasa da zai kawo muku wani da shafi tallafin karatu ga yaran ku, ko koyar da sana’o’in dogaro da kai ga matan ku, kai har ma kuɗi da kayan abinci, kada ku ƙi. Ku karva, ku shiga, ku koya, haqqin ku ne, in ba irin wannan lokacin ba, zai muku wuya ku gan shi ko kuma ya tallafa muku.

Wasu ’yan siyasar da zarar buƙatarsu ta biya to, shi kenan. An ci moriyar ganga, sai su yaɗa kyaurenta. Don haka ku yi amfani da hankalin ku, ku zaɓi ɗan takarar da ya fi cancanta, wanda ku ka fi amincewa, kuma ku ke da kyakkyawan zaton zai muku adalci da jagoranci nagari, ko da kuwa ba addinin ku ɗaya ba. Domin shi adalci ba ruwan sa da addinin da mutum ya fito.

Ba da jimawa ba ne a wajen wani babban taron Mauludi da aka gudanar a Jihar Kogi, tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya yi wani jawabi wanda a ciki ya ja hankalin ’yan Nijeriya su yi wa kansu faɗa, kada su bari a babban zave mai zuwa na 2023 a yaudare su da addini ko wani ɓangaranci, su tabbatar sun zaɓi wanda ya fi cancanta kuma suke tunanin samun adalci daga gare shi.

Allah ya ba mu shugabanni nagari, masu tausayi da jin ƙan talakawan su, waɗanda za su sa kishin qasa da tsoron Allah a zukatan su, don kyautata rayuwar ’yan Nijeriya bakiɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *