Buƙatar duba tsarin shari’ar Nijeriya

Kotu

Assalam alaikum. Yayin da a Nijeriya ake fuskantar ƙalubale da suka shafi laifukan fyaɗe da cin zarafin mata da ƙananan yara da sauran kasha-kashe marasa dalili, masana harkokin shari’a a matakai daban-daban na ganin yadda tsarin shari’ar ƙasar ya ci karo da al’adu, yanayin zamantakewa da kuma addini.

Wannan al’amarin dai ya sake kunno kai ne a daidai lokacin da ake ganin cewa masu aikata muggan laifuffuka kamar fyaɗe, cin zarrafin mata da ƙananan yara, kashe-kashen mutane na ci gaba da cin karen su ba babbaka sakamakon yadda ake ɗaukar tsawon lokaci wajen zartar da hukunci, lamarin da ke sanyaya wa waɗanda aka zalunta gwiwa har ya kai ga suna yafewa masu laifin.

A bisa ga dukkan alamu neman daidaito a sha’anin kawo ƙarshen aikata muggan laifuka a Nijeriya, ta hanyar hukunta masu aikata su na buƙatar dukannin masu ruwa da tsaki su haɗa gwiwa don warware matsalolin baki ɗaya.

A jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya, Kwamishinar Harkokin Mata a jihar, Hajiya Hauwa Baa Abubakar, ta ce a kusan dukkan gundumomin jiharta an kafa kotuna na musamman don tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka kama da aikata muggan laifuka ba tare da ɓata lokaci ba.

A can jihar Zamfara kuwa, kwamishinan shari’a kuma antoni janar na jihar Zamfara, Malam Aminu Junaidu, ya bayyana cewa musifar da ke mayar da hannun agogo baya a wajen hukunta masu aikata laifuffuka, kamar na fyaɗe da cin zarrafi shi ne yadda waɗanda aka ci zarrafinsu ke jin kunyar bada shaida a kotuna, duk da cewa gwamnatin jihar ta amince da dokar nan ta hukunta masu aikata muggan laifuffuka a wani mataki na tabbatar kawo ƙarshen wannan al’amari.

Baya ga matakan da aka yi ta ɗauka a jihohi, shin a ina ne matsalar take, fitaccen lauya barista Mainasara Kogo, ya ce tsarin shari’a da ake amfani da shi da ya saɓa wa al’adu, yanayin zamantakewa, mutunci da addinin ’yan Nijeriya na daga cikin dalilan da ya sa matsalar aikata muggan laifuffuka ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Masana a Nijeriya dai na ganin cewa kamata ya yi a bada ƙarfi ga yadda dukkannin masu ruwa da tsaki, za su hada gwiwa don fahimtar yadda lamarin yake don yin nazarin da zai kawo mafita mai ɗorewa a yaƙi da miyagun laifuffuka a ƙasar.

Wasiƙa daga MAHDI M. MUHAMMAD, 08141306201.