Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga BBC Hausa

Daga ABDULAZIZ TIJJANI (PHD)

A duk yayin da ya kasance mutum ko wata kafar sadarwa tana da mabiya da yawa, to ya zama wajibi wannan mutumin ko kafar sadarwar su yi taka tsan-tsan wurin isar da saƙwanninsu.

Tashar BBC Hausa tasha ce mai matuƙar tasiri ga rayuwar al’ummar Hausawa a faɗin Duniya ta fuskar ilimantarwa da yaɗa labarai da al’adun da suka shafi ƙabilar Hausawa. Amma ko shakka babu a waɗannan kwanakin alamu sun nuna cewa tashar tana buƙatar gyara al’amuranta ta yadda shirye-shiryenta zasu riƙa kawo gyara, ba lalacewar al’umma ba.

A kwanakin baya ne dai BBC Hausa a shafinsu na dandalin Fesbuk suka fitar da wata ƙasida da take koyar da jima’i! Wannan abin takaici ne duba da ganin cewa mutane da yawa suna karanta rubuce-rubucenku. Ƙananun yara, matasa marasa aure da masu aure, zawarawa, da tsofaffi duk suna karanta rubuce-rubucenku. Ta yaya zai zama dai-dai ku fito da waɗannan maganganu da ƙarara suke ɗauke da nau’in kalamai na gatse-gatse a kan yadda ya kamata a yi jima’i a wannan shafin naku da kowa yake karantawa?

Ba ni da ja a kan cewa kowace al’umma tana buƙatar ilimin Jima’i wanda ake kira ‘sex education’ ko sexuality education, amma isar da saƙon da ya shafi sex education dole yana buƙatar taka tsan-tsan. Wajibi ne ya zama sakon ya dace da shekaru da yanayin masu karanta shi. Sannan shi sex education ba wai kawai magana ce da ta shafi yadda ake jima’i ba. Yayin da ya kasance shafinku shafi ne da kowa yake karantawa, to ya zama lallai ya kasance duk abinda kuka rubuta ba zai zama matsala ba idan yaro dan shekara ƙasa da goma ma ya karanta. Na kuwa tabbatar babu a duniya a inda za a ce wannan rubutun naku ya dace ɗan ƙasa da shekara goma ya karanta.

Akwai ɓangarori da dama na sex education, kamar koyar da matasa yadda za su kare al’aurarsu daga zinace-zinace, shi ma sex education ne, koyar da matasa su gane canje-canjen da za su faru a jikinsu yayin da suka fara balaga da sauransu. Me zai hana ku bayar da muhimmanci a waɗannan ɓangarorin, shi kuma ɓangaren koya jima’i ku riƙa bayar da shi a matsayin keɓantaccen ɓangare (private class) wanda sai an tantance mutum zai shiga.

A cikin jaridun Turawa kamar su New York Times, BBC ta Ingilishi, CNN, Washington Post, da sauransu, wannene suke koyar da yadda ake yin jima’i ƙarara haka? 

Mun yi laifi idan muka ce ƙabilar Hausawa kawai aka raina shi ya sa ake sakin irin waɗannan rubutu gatse-gatse kowane Bahaushe komai ƙanƙantarsa ya karanta?

Gaskiyar magana ya kamata nan gaba ku kula sosai a kan yadda za ku riqa yaɗa rubuce-rubucenku. Wajibi ne ku kasance masu sauke nauyin amanar da take kanku ta tabbatar wa al’ummar Hausawa ba ta gurɓace ba. Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan duk wani wanda yake da kunnuwan da suke sauraronsa a wannan ƙabila ta Hausawa.

Al’ummarmu, musamman matsa suna matuƙar buƙatar samun sahihan bayanai dangane da al’amuran da suka shafi al’ada, daukar ciki, yadda za a guji ɗaukar ciki, yaɗuwar cututtukan da ake samu ta hanyar jima’i (sexually transmitted diseases), da yadda za a kare yaɗuwar su waɗannan cututtukan a tsakanin al’umma da sauransu. Duk waɗannan wasu reshe-reshe ne da ya kamata a ce an basu muhimmanci an koyar da al’umma su cikin nutsuwa da sanin ya kamata.

BBC Hausa za ta iya ƙaddamar da shirye-shirye na wayar da kan shugabannin al’umma a kan muhimmancin bayar da shi wannan sex education ɗin ga waɗanda suka dace a basu. ‘Yan kowace shekara akwai irin sex education din da ya kamata a sanar da su. Don haka, yana da matuƙar muhimmanci BBC su san cewa bai kamata su riƙa sakin waɗannan zantuka barkatai ba. 

Tabbas kasancewar wannan  rubutun naku ya yi zafi ƙwarai da gaske, zai iya kawo tasgaro wurin samun mutane su karɓi duk wani tsari da za ku zo da shi ta fuskar inganta shi wannan muhimmin ilimin a cikin al’umma. Amma ni a ra’ayina, lokaci bai ƙure ba. Ya kamata ku yi amfani da wannan damar da waɗannan shawarwarin wurin gyara shirye-shiryenku da suka shafi shi wannan ilimin na jima’i. 

Ya kamata ku zauna da Malamai da shugabannin al’umma da masu manyan muryoyi a cikin al’ummar Hausawa a fito da wani tsari da zai taimaka wurin yaɗa wannan ilimi a cikin al’umma ba tare da an gurɓata tarbiyyarta ba. Yan kowacce shekara akwai irin sex education din da ya kamata a sanar da su, amma galibi kuskuren da kaso mai yawa na masu ƙoƙarin koyar da wannan ilimi na sex education suke tafakawa shi ne, ba sa la’akari da shekarun masu sauraronsu. Abin takaicin kuma shi ne BBC ita ma ta shiga wannan sahun.

Don haka, shawara ta gaskiya ita ce, cewa yana da matuƙar muhimmanci BBC su san cewa bai kamata su riƙa amfani da kafofin sadarwarsu wurin isar da saqon da zai iya gurbata tarbiyyar al’umma ba.

Daga Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD – [email protected]