Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Shugaban ƙaramar hukumar Zariya

Daga MUHAMMAD AMINU IDRIS

Zuwa ga Shugaban ƙaramar hukumar. Fatan wasiƙar nan ta same ka cikin ƙoshin Lafiya. Na rubuta wannar wasiƙa zuwa gare ka ne domin na sanar da kai munanan abubuwan da suke faruwa a hanyar Ƙofar Doka zuwa Tudun Wada, dukkan a Zaria.

Wannan hanya da ta zamo mahaɗa tsakanin ƙaramar hukumar Zaria zuwa ƙaramar hukumar Sabon Gari, ta zamo wani fage dake da yawan afkuwar haɗarruka, saboda gyaran da ake yi a kanta. Kullum sai an yi haɗarruka da suke jawo raununnuka da a wani lokaci ma akan rasa rai.

Saboda a rage cinkoson ababen hawa, masu aikin hanyar sun fasa shingen da ya raba hanya a dai-dai ƙofa ta uku ta Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Tudun Wada.

Maimakon masu ababen hawa su yi amfani da kyakkyawar damar da aka ba su, sai ya zamanto suna amfani da ita wajen tuqin gangancin da yake jawo haɗarruka sosai kuma a kullum.

Na yi bincike na kusan wata shidda, daga ƙarfe shida na yamma zuwa ƙarfe takwas na dare, a kullum akan yi haɗari kamar sau biyar saboda masu motocin da suke bin “one-way” dakuma Yan achaba da ‘yan a-daidaita masu tsananin tuƙin ganganci!

Ina kira ga Mai girma Shugaban ƙaramar hukumar Zaria da ya gaggauta sa wa a rufe wannan shinge da aka buɗe domin ceton rayukan al’ummar Zaria. Kuma lallai wajibi ne a Sanya doka mai tsanani a kan masu tukin ganganci!

Shataletalen Shiri

Aikin gadar sama da ake yi, wadda yanzu aikin ya tsaya, ya sa hanyar da ake bi ta zamo wani babban ramin da yake da wahalar bi ga masu ababen hawa.

Ɗaya hanyar ma da ake bi a zagayo ta layin Sarki a ɓullo ta layin Bare-bari ko layin Nabawa ma sun zama haka. Kullun sai an yi haɗarruka a waɗannan hanyoyi su ma. Ina kira ga Maigirma Shugaban qaramar hukumar Zaria da ya taimaka ya sa a ciccike waɗannan ramuka domin ceton rayukan al’ummar Zaria.

Ina maka fatan alkhairi da kuma samun nasarori a rayuwa.

Muhammad Aminu Idiris (Fellow MLSCN & MIBMS London). Ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Zariya, Kaduna.