BUA ya saya wa Nijeriya rigakafin korona guda milyan ɗaya… da magana – inji CACOVID

Daga FATUHU MUSTAPHA

Fitaccen kamfanin nan BUA Group, ya saya wa Nijeriya maganin rigakafin cutar korona guda milyan ɗaya a matsayin gudunmawarsa ga ƙasa wajen yaƙi da annobar korona.

Bayanai sun nuna BUA ya sayi maganin ne tare da haɗin guiwar haɗakar masu taimaka wa Gwamnatin Nijeriya da saurarnsu wajen yaƙi da koro da aka fi sani da CACOVID a taƙaice.

Ana sa ran magani ya iso Nijeriya a mako mai zuwa wanda idan hakan ya tabbata, a iya cewa shi ne ya zama rigakafi na farko da Nijeriya ta samu tun bayan ɓullar annobar korona.

Kamfanin BUA ya ce kyauta za a raba wa ‘yan Nijeriya maganin ba tare da biyan ko sisi ba.

Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya nuna godiyarsa ga Bankin AFREXIM, Dr Benedict Oramah wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen sayo maganin.

Haka nan ya yaba wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) dangane da sanya ido kan sha’anin sayo maganin ta haɗin guiwar haɗakar CACOVID.

A cewar Rabiu, “BUA ya sayi maganin ne ta hanyar biyan kuɗin maganin baki ɗaya saboda a makon da ya gabata ne kaɗai aka iya samun maganin ta dalilin AFREXIM.

“Muna sa ran maganin ya iso nan da kwanaki 14 masu zuwa, inda muke fatan za a bada fifiko kan ma’aikatan da suka bada rayuwarsu wajen yaƙi da annobar.”

Ya ƙara da cewa, “BUA na da niyar ƙaro maganin har guda milyan biyar nan bada daɗewa ba ta hanyar amfani da tsarin da aka bi wajen sayen na farko.”

A wata sabuwa, biyo bayan labarin da aka yi ta yayatawa game da rigakafin cutar korona da kamfanin BUA ya saya wa Nijeriya, inda har kamfanin ya nuna cewa da taimakon haɗakar CACOVID wajen sayo maganin, sai dai CACOVID ta ce babu ruwanta a wannan batu.

Saboda a cewarta bai yiwuwa mutum guda ya sayi rigakafi daga kamfanin da ya samar da magani, don haka haɗakar CACOVID ta ce ba ta yarda da matsayar kamfanin BUA ba.

A wani bayanin ƙarin haske da ta fitar game da wannan batu na sayen maganin rigakafin korona, CACOVID ta ce wataƙila an yi wa zantukan Shugaban Kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad bahaguwar fahimta ne.

Tana mai cewa, “Bayanan ba gaskiya ba ne, saboda ita CACOVID haɗaka ce mai guadana bisa tsarin karo-karo. Babu inda aka yi wata yarjejeniya a tsakanin BUA da CACOVID da kuma Bankin Afrexim.”

Sai dai Shugaban Kamfanin BUA ya maida wa CACOVID ɗin martani, inda ya ce haɗakar ta daina siyasantar da rayukan ‘yan Nijeriya.