Buhari bai taɓa ba da umarnin cire tallafin fetur ba – Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa, ba za a cire tallafin man fetur ba a yanzu haka ba, saɓanin yadda wasu kafafen sada zumunta da na zamani suka ruwaito.

Sanata Lawan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ranar Talata a Abuja.

A cewarsa, Buhari bai taɓa bai wa kowa izinin a cire tallafin man fetur ba kamar yadda ake ta cece-kuce a wasu sassan ƙasar.

“Mun ji motsin mutanenmu. Kuma na ga ya dace in ziyarci shugaban ƙasa a matsayinsa na jagora a ƙasar, domin tattauna wannan batu da ya shafi ‘yan Nijeriya, kuma ina mai farin cikin sanar da ‘yan Nijeriya cewa shugaban ƙasa bai taɓa gaya wa kowa cewa a cire tallafin man fetur ba,” inji shi.

A cewarsa, duk da cewa tallafin da ake bai wa man fetur yana da yawa, ba za a iya tura nauyin ga talakawan ƙasa ba.

Ya ce, “na sani kuma na yarda cewa tallafin yana da nauyi sosai. Amma ina ganin ba za mu taɓa miƙa nauyin ga ’yan ƙasa ba.”

“Na yi imanin cewa muna buƙatar mu dubi adadin da aka ambata na iya zama lita miliyan 100 da mutane ke ikirarin muna cinyewa. Da gaske ne?” Ya tambaya.

Lawan ya dage cewa bai gamsu da cewa ‘yan Nijeriya na cin haka a rana ba, ya ƙara da cewa akwai yuwuwar yin zagon ƙasa a ciki.

Ya ƙara da cewa, “Abin gazawa ne idan har ba za mu iya sarrafa shi ba, wannan ɓangare na safarar man fetur na musamman shi ne man fetur sannan kuma a mayar da martani ga talakawan ƙasa.”

Lawan ya yaba wa shugaban ƙasar kan yadda yake nuna damuwa kan halin da ’yan Nijeriya ke ciki.

“Don haka, ina so in yaba wa shugaban ƙasa, saboda har yanzu kiyaye wannan falsafar na tabbatar da cewa mafi yawan talakawan Nijeriya ba sa shan wahala ta kowace hanya.

Ana nufin gwamnati ta yi wa mutane hidima. Kuma ainihin dokar gwamnati da muka sani ita ce kare rayuka da dukiyoyi da jin daɗin al’umma. Kuma wannan al’amari na tarayya wani ɓangare ne na walwala.

Mai yiyuwa ba daidai yadda muke so ba wajen aiwatar da tallafin. Amma wannan shi ne ƙalubalenmu a matsayinmu na gwamnati da kuma a matsayin gwamnati,” inji shi.

Akan kalaman da wasu gwamnonin jihohi suka yi a baya-bayan nan na neman a gaggauta cire tallafin man fetur, Lawan ya ce, “to, ra’ayinsu kenan. Da sun yi wani abu a kai.

Yanzu dole ne mu yi wani abu a kai. Na yarda cewa nauyin yana da nauyi. Amma ni ina ganin bai kamata talakan ƙasa ya ɗauki nauyi ba. Ya kamata mu a gwamnati mu taru mu nemo mafita kan hakan, ciki har da jihohin PDP. Kuma PDP a matsayinta na jam’iyyar siyasa, dole ne a samar da mafi ƙarancin matakin ɓangaranci.”

A kan sabon ƙudirin dokar zaɓe da shugaban ƙasar ya ƙi amincewa da shi, Lawan ya bayyana fatansa na cewa wata ƙila dokar zaɓen da aka yi wa kwaskwarima ta dawo wa shugaban ƙasa mako mai zuwa domin amincewa da ita.