Buhari bai tattauna batun karɓa-karɓa da ‘yan takara ba, cewar hadimin Sanata Adamu

Sanata Adamu da Tinubu

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bai tattauna batun tsarin karɓa-karɓa ba a tsakaninsa da ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na APC.

Hadimin Shugaban APC na Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Nata’ala Keffi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, labarin da ke karakaina a kafafen sada zumunta na zamani dangane da tsarin mulkin karɓa-karɓa da aka ce Buhari ya zance a kai ba gaskiya ba ne, aikin masharranta ne kawai.

Nata’ala ya ce, Shugaba Buhari cewa ya yi, “Ba tare da take cancantar kowa ba, ina kira gare ku da ku yi tuntuɓa a tsakaninku da kuma jam’iyya da zummar sasantawa don taimaka wa jam’iyya wajen rage yawan ‘yan takara, sannan a fito da ɗan takarar ɗaya da kuma kawar da ɗar-ɗar a tsakanin mambobin jam’iyya.”

Haka nan, Buhari ya nuna wa gwamnonin APC buƙatar da ke akwai na jam’iyyar ta shiga zaɓen 2023 da ƙarfinta da haɗin kai tare da gabatar da ɗan takarar da zai bai wa ‘yan Nijeriya ƙwarin gwiwa da kuma tabbatar da nasara ga jam’iyyar.

Buhari ya ba da tabbacin  cewa don cigaban ƙasa da jam’iyyar APC, zai ci gaba da kwatantan shugabanci mai nagarta har zuwa lokacin da jam’iyyar za ta tsayar da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa da kuma ƙarfafa jam’iyyar.

Don haka Shugaban ya ce, “Ina neman goyon bayanku don cin ma duka waɗnnan muhimman buƙatu.”

Nata’ala ya ce, bisa la’akari da kalaman Buhari kamar yadda suka gabata, babu inda Buharin ya ambaci batun karɓa-karɓa. Don haka ya ce ana kira ga ‘yan ƙasa da su yi yi fatali da rahoton da ya nuna Buhari ya yi magana a kan tsarin karɓa-karɓa dangane da mulkin ƙasa.