Buhari da Badaru sun jajanta kan rasuwar Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulƙadir

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, sun nuna alhininsu da kuma jajantawa dangane da rasuwar Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya fitar Buhari ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin nagartattun sarakunan gargajiya da ake da su a faɗin Nijeriya, waɗanda suka janyo wa harkar sarauta martaba.

Buhari ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda ya yi wa talakawansa hidima da gaskiya ba tare da nuna son-kai ba, wanda kuma masarautarsa ba za ta taɓa mancewa da shi ba.

Haka nan, Shugaban Ƙasar ya jajanta wa Gwamnatin Kano da Masarautar Gaya da iyalan marigayin game da wannan babban rashin, kana ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma ba shi ladan kyawawan ayyukansa.

Shi ma Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya miƙa ta’aziyyarsa ga takwaransa na Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, dangane da rasuwar Sarkin Gaya.

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Habibu Nuhu Kila, Gwamna Badaru ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga Masarautar Gaya, ga Gwamnati da al’ummar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, ya ce marigayin alama ne na zaman lafiya wanda shugabancinsa ya haifar da kyakkyawar mu’amala tsakanin talakawansa da maƙwabtansu.

Daga nan, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin da rahma, kana Ya bai wa iyalan marigayin, al’ummar Masarautar Gaya da ma jama’ar Kano kwata haƙuri da juriyar wannan rashi.