Buhari da Lawan sun nuna alhininsu kan haɗarin jirgi a Abuja

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan haɗarin jirgin saman sojoji da ya auku Lahadin da ta gabata a Abuja.

Sanarwar da hadimin Buhari kan sha’anin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, ta nuna yadda Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘yan’uwa da abokan aikin sojojin da suka rasu a haɗarin.

Sanarwar ta ce Buhari ya bi sawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya da ma al’ummar Nijeriya baki ɗaya wajen makokin jami’an rundunar waɗanda ajalinsu ya cim musu a bakin aiki.

Buhari ya ce an soma gudanar da bincike domin gano sababin haɗarin, tare da bada tabbacin cewa kula da sararin samaniyar Nijeriya abu ne da gwamnatinsa ta bai wa muhimmanci.

Daga nan, shugaban ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalai da ‘yan ƙasa haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

A hannu guda, shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya miƙa ta’aziyyarsa a bisa wannan rashi ga iyalai, Rundunar Sojin Sama da ma ƙasa baki ɗaya. Lawan ya yi haka ne ta hannun mai ba shi shawara a fannin yaɗa labarai, Ola Awoniyi.

Sanata Lawan

Lawan ya yi kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su hana aukuwar makamancin haka a gaba ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace.