Buhari da mai ɗakinsa sun bar Abuja zuwa Daura

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bar babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin bayan da ya halarci rantsar da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tunubu a dandalin taro na Eagle Square a Abuja.

Jirgin tsohon shugaban ƙasar ya ɗaga sama da misalin ƙarfe 12 na rana zuwa mahaifarsa, Daura, a jihar Katsina.

Jirgin saman sojojin Nijeriya mai lamaba 5N FGW ne ya ɗauke shi.

Buhari yana tare da maiɗakinsa, Aisha Buhari da kuma ɗansa Yusuf sai kuma kaɗan daga cikin masu yi masa hidima.

Majiyar Manhaja ta ƙara da cewa, jim kaɗan bayan tashin jirgin tsohon shugaban, wani jirgin sojojin sama mai lamba 5N-FGZ ya tsahi ɗauke da iyalansa da kuma wasu masu taimaka masa inda za a raka shi zuwa mahaifarsa Daura.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo da matarsa gami da shugaban ma’aikatansa Ibrahim Gambari, sai kuma tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello na daga cikin waɗanda suka raka tsohon shugaban zuwa wajen da ya hau jirgi, kamar yadda jaridar The nation ta rawaito.

Sauran ‘yan rakiyar sun haɗa tsohon Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, tsohuwar Ministan Jinƙai da Walwalar Jama’a, Sadiya Farouq da kuma Shugaban Hukumar Kwastam, Hammed Ali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *