Buhari ga Bankin Musulunci: ’Yan Nijeriya za su samar wa kansu aikin yi idan kun raya ƙasar

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya gana da Shugaban Bankin Cigaban Musulunci (IDB), Dakta Mohammed Al-Jasser, a gefen taron Paris kan Zama Lafiya, inda ya bayyana cewa, matuqar bankin ya taimaka wajen raya Nijeriya ta fuskar gudanar da manyan ayyuka, to ’yan ƙasar za su iya samar da kansu ayyukan yi. Don haka ne ya ce, wannan ne dalilin da ya sa gwamnatinsa ta duƙufa wajen farfao da manyan ayyukan cigaba a Najeriya.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a sanarwar da Mai Taimaka Wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labari, Mista Femi Adesina, ya yi ranar 11 ga Nuwamba, 2021.

“Muna faɗi-tashi mai wahalar gaske, don samar da manyan ayyukan cigaba, saboda ba za a taɓa samun ɗorewar cigaba ba tare da shi ba,” cewar Shugaban.

“Idan aka yi la’akari da girman ƙasarmu, muna da buƙatar hanyoyin mota, layin jirgin ƙasa, lantarki, filayen jiragen sama da gidaje, kuma waɗannan sune abubuwa da muka sa kanmu, don samar da su a shekaru shida da suka shuɗe.

“Kuma al’ummarmu suna ganin cigaban da muke samarwa daga ɗan abinda muke da shi a hannu da bai taka kara ya karya ba. Ba mu aikata wani mugun aiki da su ba. Da zarar an samar da manyan ayyukan cigaba, al’ummarmu za su riƙe kansu.”

Shugaba Buhari ya gode wa Bankin Cigaban Musulunci na IDB kan tallafi da ya ke yi kawo yanzu, inda ya ce, “abinda ya sa mu ke dogara kan ɗanyen mai, wanda hakan ya samu koma-baya sosai a lantarki. Sannu a hankali mu na kan dawowa tafarki, kuma muna samun damar numfasawa kaɗan-kaɗan cikin ƙwarin gwiwa. To, amma duk da haka muna sa ran ƙara samun haɗin kai daga gare ku.”

Dakta Al-Jasser ya ce, ya yi farin cikin kan matakin haɗin kai da ke tsakanin Najeriya da Bankin Cigaban Musulunci na IDB tun bayan da ya fara aiki watanni uku da suka gabata, kuma ya faɗa wa Shugaba Buhari cewa, “na gamsu da irin tsare-tsarenka kan manyan ayyukan cigaba, wanda hakan zai samar da damarmaki masu yawa ga matasa da ƙarfafa gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu. Najeriya ƙasa ce da ta ke taimaka mana, kuma da dace da dukkan taimako da za ta iya samu.”

Shugaban na IDB ya ce, “babban aikin bankin shine ɗabbaƙa ayyukan cigaba a tsakanin mahukunta, kuma za mu ci gaba da karkata hannayenmu na taimako ga Najeriya.”