Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI
Kamar yau ne muka cika da murnar rantsar da Shugaba Buhari a matsayin sabon Shugaban ƙasar Nijeriya a shekarar 2015. Wasu sun zuba ruwa a ƙasa sun sha, don murna. Wasu sun yi wanka da kwata don murna. Wasu sun yi tattaki tun daga Legas zuwa Abuja don murna. Wasu sun yi yanke-yanken dabbobi irin su shanu da raguna da kaji, gwargwadon dai ƙarfin mutum. Wasu sun yi rawa da waƙa a titi don kawai murnar rantsar da sabon Shugaban ƙasa Buhari a 2015.
Tun a farkon shekarar mulkinsa wasu suka fara dawowa daga rakiyarsa. Wasu kuwa suna nan daram daƙam. Wadanda suka fara fita a rakiyarsa sai suka zama mujiya. ba su Isa suyi Wani tari ba yanzun nan za a kafurta su. Daga ƙarshe da tafiya ta fara tafiya, sai aka fara samun kaso mai ɗan kauri suna dawowa daga rakiyarsa.
Kafin zaɓen da zai maimaita zama Shugaban ƙasa karo na biyu. Mutane da yawa sun dawo daga rakiyarsa. Amma duk da haka, ba su kai masoyansa yawa ba. Sai dai a lokacin ana ɗaga musu ƙafa ba a kafurta su sai dai a ce musu ‘yan Shi’a, sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin ‘Yan Shi’a da Shugaban Sojoji Burutai har ta kai da zubar da jinin dubban mutane.
A zangon mulkin Buhari karo na biyu, da yawa waɗanda suka yi sake yin jam’iyyar karo na biyu ko kyauta ko murna don sake dawowar mulkin Buhari a karo na biyu. Su kansu a lokacin sun jigata da yawansu sun bar tafiyar saboda tsaurin da mulkinsa ya yi a karo na biyu Wanda ya zarce ba baya. Hatta a Soshiyal Midiya kaso 85 cikin 100 duk sun bar tafiyarsa. Wanda da su ne masu kafurta mutum idan ya ce ya daina tafiyar Buhari.
Yau cikin hikimar Allah har an shekara takwas! Wasu da yawa da suka ga farkon mulkinsa ba su ga ƙarshen mulkinsa ba. Allah ya gafarta musu. Amin summa amin.
Babban Darasin da mulkin Buhari ya koya wa mutane shi ne; Tawakkali da Kuma rayuwa a kan abinda ya zo hannunka ko Kuma kake da shi. (illa ƙalilan ne kawai da ba su ɗauki wannan darasin ba).
Abinda ya zama haɗakar ga kowa ga mulkin Buhari suna da yawa. Amma kaɗan daga cikinsu su ne;
- Tsadar kayan masarufi
- Cire tallafin man fetur
- Ƙarin kuɗin haraji (VAT) na komai har da kuɗin kiran waya da data.
- Yajin aikin Jami’o’i da ƙarin kuɗin karatun kansa.
- Ƙarin farashin Dala.
- Satar mutane da sauran kashe-kashe.
Na ƙarshe-ƙarshen nan wanda sai da kowa ya ji a jikinsa shi ne;
- Canjin fasalin kuɗin Nijeriya (wato sabon kuɗi da aka canja). Kowa ya sha wahala. Da mai kuɗi da talaka.
A ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Allah ya kawo ƙarshen wa’adin mulkin Buhari a Nijeriya. Wannan kaɗai ya ishi Ɗan’adam ishara. Ya zauna ya nutsu ya san cewar; komai ya yi farko zai yi ƙarshe.
Daga ƙarshe, muna addu’a ga sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Alhaji Bola Ahmad Tinibu Allah ya sa ya zama shugaba adali Wanda zai yi mulkin Nijeriya babu ƙabilanci ko nuna wariya ga wani yanki. Allah ya ba shi ikon yin adalci ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Abdullahi Jibril Larabi (Larabi Larabeen), marubuci ne, kuma ɗan ƙasa mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga jihar Kano.