Buhari na ganawa da shugabannin tsaro

Daga BASHIR ISAH

Yanzu haka Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana kan tattaunawa da shugabannin fannin tsaro a fadarsa da ke Abuja.

Taron wata dama ce da za ta bai wa Buhari zarafin jin yadda harkokin tsaron ƙasa ke gudana daga bakin jagororin fannin.

Mahalarta taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Mai Bai wa Buhari Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Major General Babagana Monguno (rtd), Shugaban Tsaro, General Leo Irabor.

Sai kuma shugaban sojojin ƙasa, na ruwa da na sama haɗa da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba, duk suna cikin taron.

A tare mu a gaba don jin sakamakom taron…