Buhari ne zai bayyana matsaya ta ƙarshe kan makomar Abba Kyari – Dingyaɗi

Daga SANI AHMAD GIWA

Ministan Lamuran ‘Yan Sandan Nijeriya, Muhammad Maigari Dingyaɗi ya ce sun kammala bincikensu kuma tuni sun miƙa shawarwari da suka bayar ga hukumomin da ya kamata.

Ministan ya ce Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne zai yanke matsaya ta ƙarshe kan matakin da za a ɗauka a kan DCP Abba Kyari, da wata kotun ƙasar Amurka ta buƙaci a kamo mata shi, bisa tuhumarsa da alaƙa da Hushpuppi.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels, Dingyaɗi ya ce gwamnatin Nijeriya na buƙatar ganin an yi duk abin da ya kamata akan lamarin Abba Kyari, kasancewar yana da alaƙa da matakin ƙasa da ƙasa.

Ya ce kamar yadda kowa ya sani ne rundunar ‘yan sandan ƙasar ta kafa wani kwamiti domin yin cikakken bincike akan dukkan zarge-zargen da ake yi wa Kyari, kuma tuni da kwamitin ya kammala aikinsa tare da miƙa rahotonsa ga babban Sufeto Janar na ‘yan sanda.

Ministan ya ce haka kuma an gabatar da rahoton kwamitin da shawarwarin da ya bayar ga ministan shari’a na ƙasa domin jin ra’ayinsa, a yayin da kuma ita ma ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, za a gabatar mata da rahoton, kafin ɗaukar mataki na ƙarshe akan lamarin.

“Abin da ya kamata ‘yan Nijeriya su sani shi ne, hukumomin ‘yan sanda sun yi na su aiki kamar yadda ya kamata, kuma a bayyane suka gudanar da komai. Abin da ya rage yanzu shi ne Shugaba Muhammadu Buhari ne zai yanke shawarar matakin da za a ɗauka akan lamarin,” inji Maigari Dingyaɗi.

Rundunar ‘yan sandan ƙasar dai ta dakatar da Abba Kyari daga muƙaminsa tare da maye gurbinsa, biyo bayan zarginsa da alaƙa kan badaƙalar zambar kuɗi ta yanar gizo da ake yi wa wani ɗan Nijeriya Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi a ƙasar Amurka.

Alqalin wata kotu a jihar California ta ƙasar Amurka, Otis Wright, ya baiwa hukumar binciken Amurka ta FBI umarnin kamo Abba Kyari da kuma gurfanar da shi a gaban ta a can ƙasar ta Amurka, domin amsa tuhumar da ake yi masa.