Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira ƙarƙashin kulawar Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Yayin ƙaddamarwar wadda ta gudana a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin, Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnan CBN, Mr. Godwin Emefiele, bisa wannan cigaba na samar da sabon tsarin hada-hadar kuɗi a ƙasa.

A nasa ɓangaren, Mr. Emefiele ya sanar da samuwar wani sabon tsarin kasuwanci mai suna “The 100 for 100 PPP – Policy on Production and Productivity,” wanda a cewarsa tsarin zai taimaka wa ƙasa gaya wajen rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙetare.

Emiefele ya ce sabon tsarin zai gudana ne ƙarƙashin Sashen Bunƙasa Kuɗaɗe kuma ƙarƙashin kulawarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *