Buhari ya ƙaddamar da kwamitin shirin raba ‘yan Nijeriya miliyan 100 da fatara

Daga UMAR M. GOMBE

A Talatar da ta gabata ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kwamitin da aka ɗora wa alhakin sanya ido kan shirin rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ana sa ran ya raba ‘yan Nijeriya miliyan 100 da fatara.

Buhari ya sha alwashin gwamnatinsa za ta fito da dabarun da za su taimaka mata wajen kuɓutar da ‘yan Nijeriya milyan 100 daga ƙangin talauci a tsakanin shekaru goma masu zuwa.

A jawabinsa yayin ƙaddamar da kwamitin, Buhari ya bayyana dabarar da kwamitin NPRGS za ta bi wajen yin wannan aiki. Tare da cewa an soma gudanar da aikin ne tun a Janairun 2021 a lokacin da ya nemi majalisar mashawartansa kan tattalin arziki su lalubu hanyar kawar da fatara a tsakanin ‘yan Nijeriya.

An rawaito Buhari ya ce za a yi gyara duk kura-kuren da aka tafka a baya wajen samar da tsarin da zai azurta miliyoyin ‘yan ƙasa.

Buhari ya ba da misali da ƙasar Indiya inda ya ce, “Idan Indiya za ta iya kuɓutar da mutum miliyan 271 daga ƙangin talauci tsakanin 2006 da 2016, tabbas Nijeriya ma za ta iya raba mutum miliyan 100 da fatara a cikin shekaru goma.”

Mambobin kwamitin sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da gwamnonin Delta, Ekiti, Nasarawa, Sakkwato, Barno da na Ebonyi.

Sauran sun haɗa da ministocin Tattalin Arziki, Harkokin Noma, Kiwon Lafiya, Ilimi, Agaji da Jinƙai, Kwadago da na Masana’antu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *