Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun N200, N500 da N1000

Daga WAKILINMU

A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1000 bayan sake musu fasali.

Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira ɗin ne a wajen taron Majalisar Zartarwa a Abuja.

Idan za a iya tunawa, ranar 26 ga Oktoba n 2022, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba da sanarwar shirin Gwamnatin na neman sake fasalin takardun kuɗin da lamarin ya shafa.

Tare da cewa, an ɗauki matakin hakan ne domin kula da kuɗaɗen da ke hannun ‘yan ƙasa ana hada-hada da su.

CBN ya ce tsaffin takardun Naira da aka sauya wa fasalin za su ci ga da aiki har zuwa 31 ga Janairun 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *