Buhari ya ƙara farashin fetur zuwa N179 a asirce

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi ƙarin kuɗin fetur ba tare da sanarwa ba, inda a yanzu ta amince a sayar da lita ɗaya na fetur a kan N179 maimakon N165 da aka sani a baya.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da kamfanin mai na NNPC Limited ya miƙa wa dillalan mai tare umartan su a kan su sauya nasu farashin daga yau Talata, 19 ga Yuli, 2022.

Wannan na zuwa ne bayan da matsalar ƙarancin fetur ta sake kunno kai a ƙasar wanda hakan ya sanya ‘yan kasuwar mai ɗin ke ta sayar da man a kan farashi mabambanta.

Idan za a iya tunawa, a baya Ƙungiyar Dillan Fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta fito ta bayyana cewa, duba da yanayin kasuwar fetur a yanzu mawuyacin al’amari ne su iya ci gaba da sayar da fetur a N165 kan kowace lita.

Bisa wannan dalili ne hukumar kula da sha’anin haƙo fetur ta ƙasa ko kuma NMDPRA a taƙaice tare da ‘yan kasuwar suka ƙara farashin man zuwa tsakanin N170 da N190 kan lita ɗaya.

Bayanai sun ce hakan ya tabbata ne sakamamakon ganawar da ɓangarorin biyu suka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Wata majiya ta ce, a wajen taron ne aka cim ma matsayar ƙarin farashin man, sannan aka buƙaci mahalarta taron kowa ya kame bakinsa.

Majiyar ta ƙara da cewa, a wajen taron aka halasta wa gidajen mai na cikin birane sayar da mansu tsakanin N165 zuwa N175 kan kowace lita, sannan waɗanda ke wajen gari kuma N189.