Buhari ya ƙirƙiro cibiyar kula da tu’ammali da ƙananan makamai

Daga AISHA ASAS

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da batun ƙirƙiro Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai ta Ƙasa (NCCSALW) wadda za ta kasance ƙarƙashin kulawar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro.

NCCSALW ita ce cibiyar da za ta yi aiki a madadin Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Kula da Ƙananan Makamai da aka rusa. Har wa yau, za ta kasance cibiya ta bincike, yin dokoki tare da sanya ido kan harkar ƙananan makamai a Nijeriya.

Tuni Shugaba Buhari ya naɗa Major General AM Dikko (Rtd) a matsayin Kodinetan da zai kula da cibiyar.

Sanarwar da ta fito ta hannun Shugaban Sashen Sadarwa na Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’nin Tsaro, ZM Usman, ta nuna ɗaukar wannan mataki wani ɓangare ne na ƙokarin da Gwamnatin Tarayya ke wajen sake wa fannin tsaron ƙasa fasali tare da inganta shi domin iya magance matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa.

Sanarwa ta ce yadda ake tu’ammali da ƙananan makamai a tsakanin ƙasashen Afirka hakan ya yi matuƙar tasiri wajen haifar da ta’addanci, safarar mutane, manyan laifuka da makamantansu a yankin Afirka ta Yamma da ma Nijeriya.

Don haka gwamnati ta ce sabuwar cibiyar za ta yi aikinta ne daidai da dokokin ECOWAS ta hanyar sanya idanu da kuma lura da yadda ake shigarwa da fitar da ƙananan makaman har ma da ƙera su.