Buhari ya ƙaddamar da aikin layin dogo daga Kano Zuwa Nijar

Daga BASHIR ISAH

A Talatar da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin gina layin dogo wanda zai tashi daga Kano-Katsina-Jibiya-Maraɗi, da kuma wanda zai ratse zuwa Dutse a jihar Jigawa.

Da yake jawabi ta bidiyo daga fadarsa da ke Abuja yayin bikin ƙaddamawar, Buhari ya ce bayan kammala aikin hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arzikin ƙasa musamman ma hada-hadar kasuwanci a tsakanin Nijeriya da Nijar.

Daga nan ya kira ga ‘yan kasuwa da su yi amfani da wannan dama wajen gudanar da harkokin kasuwancin da ba su saɓa wa dokoki ba da nufin bunƙasa tattalin arzikin kasa.

Bikin ƙaddamar da aikin ya guda ne a ƙauyen Kwarin Tama a jihar Katsina, inda ya samu mahalarta daga sassa daban-daban ciki har da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, da Ministan Harkokin Cikin Gida, Ministan Labarai da al’adu, Ministan Harkokin Waje, Gwamnan Katsina da na Jigawa da na Maraɗi a Nijar, da dai sauransu.


Ana sa ran samar da layin dogon ya zama wata mahaɗa tsakanin wasu jihohin Arewa uku, wato Kano, Katsina, da kuma Jigawa, sannan ya ƙarasa a Maraɗin Nijar.

Kazalika, ana sa ran samuwar hanyar ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya kasancewar harkokin shigar da fitar da kayayyaki daga Ƙasar Nijar za su kankama.