Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen kwamishinonin INEC da zai naɗa

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura sunayen mutane shida da ya ke so ya naɗa a matsayin kwamishinonin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ga Majalisar Dattawa domin ta amince da zaɓen su da ya yi.

Sun haɗa da Lauretta Onochie, wadda ita ce mai ba shi shawara ta musamman kan soshiyal midiya.

A da dai majalisar ta yi fatali da zaɓin da ya yi wa Onochie a zaman ta na ranar 12 ga Oktoba, 2020 domin wasu sanatoci sun ce ba su amince da naɗin nata ba.

A zaman majalisar na ranar Laraba ta wannan makon, Sanata Yahaya Abdullahi (ɗan APC daga mazaɓar Kebbi ta Arewa) ya karanta takardar musamman da Buhari ya aika wa majalisar, inda ya nemi amincewar ta a zauren majalisar, ya ce:

“Ana so Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar mai girma Shugaban Ƙasa kan batun tabbatar da naɗin waɗannan mutane a matsayin kwamishinoni na Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kamar yadda sakin layi na 14 sheɗarar I(F) na bugu na uku na kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanadar.

“Waɗanda aka zaɓan su ne: Farfesa Muhammad Sani Kallah (Kwamishina, Katsina); Lauretta Onochie (Kwamishina, Delta), Farfesa Kunle Cornelius Ajayi (Kwamishina Ekiti); Sa’idu Ɓaɓura Ahmad (Kwamishina, Jigawa); Farfesa Sani Muhammad Adam (Kwamishina, Arewa ta Tsakiya) da Dakta Baba Bila (Kwamishina, Arewa ta Gabas).’’

Sai dai Sanata Enyinnaya Abaribe (PDP-Abia), wanda shi ne shugaban marasa rinjaye, da shugaban majalisar ya neme shi da ko zai goyi bayan roƙon na shugaban ƙasa, ya yi nuni da cewa ai kuwa a da can baya majalisar ba ta amince da zaɓin Lauretta Onochie ba.

Jin haka, sai shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, a amsar da ya bayar, ya miƙa batun naɗe-naɗen baki ɗaya ga Kwamitin INEC na majalisar domin su bada shawara kan abin da doka ta ce, kuma su kawo rahoto nan da mako biyu.