Buhari ya aike da saƙon bidiyo Zamfara bayan hazo ya hana shi zuwa jaje

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke ziyararsa zuwa jihar Zamfara a jiya Alhamis sakamakon rashin kyawun yanayi da ya jawo hazo, inda ya aike da wani saƙon bidiyo, domin nuna alhininsa da rashin jin daɗinsa sakamakon rashin zuwa yi musu jajen abubuwan da ke faruwa na matsalolin tsaro a jihar.

A cikin bidiyon mai tsawon minti 1:30 da aka nuna shugaban ya na magana a jiya da daddare, a ciki ya ce, “ban ji daɗin abin da ya afku ba, saboda na yi niyya daga Sakkwato na zo nan Gusau na gaida ku, na yi mu ku jajen abubuwan da suke afkuwa, amma hunturu… saboda ba a gani, sai kuma ga iska, shi ya hana, ban samu damar zuwa ba.

“Gwamnanku da shi da ’yan majalisarshi da kwamishinoninshi sun yi tsari ƙwarai da gaske na zuwana, amma Allah bai yi ba. Sai a yi haƙuri. In sha Allahu zan jira lokacin da zan samu damar zuwa, idan yanayin ƙasa ya gyaru.

“Sojoji da ’yan sanda da sauran masu tsaron ƙasa, da ikon Allah za su tashi tsaye su yi maganin masu ta’adda. Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Zamfara su na iyaka ƙoƙarinsu su tabbata zama lafiya ya tabbata a Zamfara. Mu na fata za ku bada haɗin kai ta hanyar sanar da hukuma su waye ’yan ta’adda, don a yi maganinsu. Na gode gode ƙwarai da gaske. Allah ya tabbatar mana da alheri.”

Buhari ya ɗage ziyarar ce bayan saukarsa a makwabciyar Jihar Zamfara, wato Jihar Sakkwato, inda ya ƙaddamar da aikin gina masana’antar siminti ta kamfanin BUA.

A yayin da ake jiran Buhari ya ƙarasa zuwa Jihar Zamfara, gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya sanar cewa rashin kyan yanayin sararin samaniya ya hana jirgin shugaban ƙasar tashi daga Sakkwato, wanda ya tilasta ɗage ziyarar tasa zuwa Zamfara.

“Shugaban Ƙasa ya yi magana da ni inda ya buƙaci in isar da saƙon ban haƙurinsa ga al’ummar Jihar Zamfara. Amma ya ce, zai sake sa ranar zuwa jihar a makonni masu zuwa, wanda za a sanar a nan gaba,” inji Gwamna Matawalle.

Sanarwar ta fito ne a yayin da mutanen Jihar Zamfara suka yi dafifin jiran isowar Buhari wanda ke hanyarsa ta kawo musu ziyarar ta’aziyya.

Buhari ya shirya kai ziyarar ce domin jajanta wa al’ummar jihar game da asarar rayukan da aka yi a sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Gabanin ziyarar tasa da aka sa rai zai kai a ranar Alhamis, an tsara Shugaba Muhammadu Buhari zai sauka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a wata ziyarar wuni guda da zai kai.

Tun a jajiberin ziyarar gwamnatin Zamfara ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta tsawon sa’a uku a yayin ziyarar ta shugaban ƙasa.

Gwamnatin jihar dai ta ce shugaban na Nijeriya zai je Zamfara ne domin jajanta wa al’ummar jihar game da miyagun hare-haren ’yan fashin daji na baya-bayan nan musamman a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Kwamishinan Yaɗa labarai na jihar Zamfara, Malam Ibrahim Magaji Dosara, ya shaida wa manema labarai cewa, tuni suka kammala shirye-shiryen tarbar shugaban ƙasar.

Ya ƙara da cewa, baya ga ta’aziyya da jajen da Shugaba Buhari zai yi wa al’ummar ta Zamfara, zai kuma ƙara wa sojoji Nijeriya da ke jihar kwarin gwiwa a kan irin samame da sauran ayyukan da suke yi wajen fatattakar ’yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohi.

Kwamishinan Yaɗa labaran ya ce, ɗaya daga cikin manufar ziyarar shugaban ƙasar a Zamfara ita ce domin ya sanyaya zukatan al’ummar ta Zamfara tare da nuna musu cewa yana tare da su.

Malam Ibrahim Dosara ya ce, “ba jajen Anka da Bukkuyum kaɗai Shugaba Buhari zai yi ba, zai yi jaje ne ga dukkan iyalan waɗanda suka rasa wani nasu a hare-haren ’yan bindigar a jihar ta Zamfara.”

A cewarsa, a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai gana da jami’an tsaron da ke aiki a jihar da malamai da sarakunan gargajiya da kuma iyalan waɗanda suka rasa ransu a yayin hare-haren.

Tuni dai gwamnatin jihar ta buƙaci al’ummarta da su kiyaye da dukkan wasu dokoki a yayin ziyarar shugaban ƙasar.

Al’ummar jihar da ma wasu a sauran jihohi sun jima suna tsokaci a kan rashin zuwan shugaban Nijeriya Zamfara don jajantawa al’ummar jihar a kan irin masifar da suke gani ta hare-haren ’yan bindiga.

Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya musamman a yammacin ƙasar da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da satar mutane abin da ala tilas mazauna yankuna da dama na jihar suka bar muhallansu don tsira da ransu.

Kusan ƙananan hukumomin jihar na fuskantar waɗannan hare-hare, inda hatta noma ma a wasu yankunan aka daina saboda yadda ’yan bindiga ke kai wa manoma hari su kashe su a cikin gonakinsu.