Buhari ya amince da kashe bilyan N18 don gina sabbin jami’o’i huɗu a sassan ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe kuɗi Naira biliyan 18 domin gina jami’o’in ƙwararru guda huɗu a faɗin ƙasa.

Gwamnati ta bayyana haka ne a Litinin da ta gabata, inda ta ce jami’o’in da za a gida sun haɗa da ta fasaha da za a gina Jigawa da Akwa Ibom, sai kuma ta kiwon lafiya da nazarin ingancin abinci da magunguna da za a gina a Azare, jihar Bauchi da Ila Orangun, jihar Osun.

Da yake yi wa manema labarai bayani a Abuja, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce jami’o’in fasaha guda huɗun da ake da su a Yola da Akure da Owerri da kuma Neja, za a ɗaga darajarsu sannan za a gina sabuwar Cibiyar Fasaha ta Ƙasa (NIT) a Abuja ya zuwa 2022.

Adamu wanda Babban Sakatare a ma’akatar, Sonny Echono ya wakilta, ya ce buƙatar gina babbar cibiyar a Abuja da kuma guda-guda a kowace shiyyar siyasa, na mazaunin cika alƙawarin da gwamnati ta yi ne.

Ministan ya ce buƙatar gina jami’o’in nazarin kiwon lafiyar ta taso ne duba da ƙarancin likitoci da kuma cibiyoyin binciken magungunan da ake fama da shi.

Ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Ma’aikatar Lafiya, Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Hukumar Birnin Tarayya Abuja da kuma sauran hukumomin da abin ya shafa wajen tabbatar da ƙudirin gwamnati na gina jami’o’i da cibiyoyin ba tare da wani tsaiko ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *